Hadura 5 na daura hotunan yaranka a shafukan ra'ayi da sada zumunta

Hadura 5 na daura hotunan yaranka a shafukan ra'ayi da sada zumunta

Allah (SWT) ya siffanta yaran da ya bamu a matsayin kwalliyan rayuwar duniya a surori daban-daban cikin Al-Kur'ani mai girma. Hakazalika mun ga yadda mutane ke nuna matukar soyayya ga yaran da Allah ya azurtasu da shi.

Iyaye na dukkan abinda zasu iya wajen kare mutuncin yaransu amma kuma sukan garzaya shafukan ra'ayi da sada zumunta da ke zagawa duniya.

Karanta hadura biyar na daura hotunan yara cikin gida a shafukan ra'ayi da sada zumunta a wannan zamani:

1. Hadarin Mazinata da masu lalata yara

Daura hotunan yara a shafukan ra'ayi da sada zumunta musamman kyawawan hotuna kan jawo hankalin masu mugun tunani inda za su rika yiwa yara kallon sha'awa wanda zai kaiga jefa rayukan yara cikin hadari

2. Yan Kungiyar Asiri

A zamanin yanzu da yan kungiyar asiri ke amfani da kananan yara wajen gudanar ayyukan shaidancinsu, daura hotunan yara a shafukan sada zumunta musamman lokacin murnar zagayowar ranar haihuwansu kan saukakewa masu kungiyar asiri sacesu musamman idan a lokacin suna bukatar yara masu shekaru na musamman. Hakan ya faru a jihar Legas inda ake sace yara yan shekaru 4 da haihuwa.

3. Yan fashi

Daura hotunan yaranka da suka dauka cikin gidanka babban dama ne ga masu fashi da makami wajen ganin irin arzikin da kake dashi cikin gidanka. Hakan zai iya jawo hankalinsu su kawo hari.

KU KARANTA: Yaki da Iran zai durkusar da tattalin arzikin duniya - Yarima MBS

4. Masu garkuwa da mutane

Daura hotunan yara a shafukan ra'ayi da sada zumunta musamman idan iyaye suka kai yaransu shakatawa kan baiwa masu garkuwa da mutane daman tunanin irin arzikin da ka mallaka kuma suyi tunanin kawo hari.

Hakazalika za su iya amfani da wannan hotunan wajen bin yaran har makarantunsu.

5. Mahassada da kambun baka

Illar Idanun mahassada da masu kambun baka abune wanda ya tabbata a addini da kuma zamantakewar yau da kullum, saboda haka, ya kamata mu kiyaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel