Aliko Dangote ya na so kamfanoni su rika ba shinkafa babban muhimmanci

Aliko Dangote ya na so kamfanoni su rika ba shinkafa babban muhimmanci

Shugaban babban kamfanin nan na Duniya na Dangote Group watau Alhaji Aliko, ya bayyana cewa zai so gwamnatin kasar nan ta wajabtawa kamfanoni gyara shinkafar da ake ci a Najeriya.

Aliko Dangote ya na neman yadda za a kare shinkafar da jama’a ke yawan ci da safe, da rana har da dare . A cewarsa cin shinkafa za ta taimaka wajen rage matsalar duk wasu cututtuka.

Mai kudin Afrikan ya na ganin cin shinkafar zai taimaka da sinadaran da ake bukata wajen gina jiki. Yanzu haka a Najeriya akwai kananan yara sama da miliyan biyu da ke fama da tamowa.

“A gidauniyar Aliko Dangote, mu na da wani tsari da mu ke kira “Nutrition Integrated Programme”, da mu ke da niyyar raba yara miliyan biyu daga rashin isasshen abinci mai lafiya.”

KU KARANTA: Aminin Jonathan ya watsawa PDP kasa a ido a Kudancin Najeriya

Babban Attajirin na Afrika ya cigaba da cewa: “Yanzu haka, mu na shirin sheke ton miliyan guda na shinkafa, shinkafar mu za ta zo dauke da wadannan sinadarai na bitamin masu bada lafiya.”

“Babban abin da ake ciki a Najeriya shi ne shinkafa, mutane na cin shinkafa da safe, su ci da rana, su ci shinkafa da dare. Don haka mu ke so gwamnati ta tsare shinkafa.” Inji Aliko Dangote.

Aliko Dangote ya yi amfani da wannan dama wajen fadawa Duniya shirin da kamfaninsa ke yi game da harkar sukari a Najeriya. Dangote ya kuma yabawa kokarin Bill da Melinda Gates a taron

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel