Masu yi don Allah: Wani mutum ya bayar da gudunmawar $1m ga cibiyar Sheikh Ibrahim Saleh, ya nemi a boye sunansa

Masu yi don Allah: Wani mutum ya bayar da gudunmawar $1m ga cibiyar Sheikh Ibrahim Saleh, ya nemi a boye sunansa

Wani mutum da ya nemi a boye sunansa, ya bayar da gudnmawar dalar Amurka miliyan daya ga cibiyar addinin Islama ta Sheikh Ibrahim Saleh.

An sanar da hakan ne a wurin taron nema agajin kudi da cibiyar ta gayyaci gwamnatoci, attajirai, 'yan kasuwa da 'yan siyasa wanda aka gudanar ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba, a Abuja.

Gudunmawar da mutumin ya bayar ita ce ta biyu ma fi tsoka a cikin sauran dumbin gudunmawar makudan kudin da jama'a suka bayar.

Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabi'u, shugaban rukunin kamfanonin BUA, shine ya bayar da gudunmawar kudi ma fi tsoka a wurin taron, inda ya bayar da gudunmawar miliyan N500.

Attajirin ya ce ya bayar da gudunmawar ne amadadinsa da iyalinsa, tare da kara bayar da tallafin miliyan N50 amadadin mahaifinsa, marigayi Sheikh Isyaka Rabi'u.

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayar da gudunmawar miliyan N25, a yayin da gidauniyar Aliko Dangote ta bayar da gudunmawar miliyan N100. Aliko Dangote ya ce ba zai bayyana wa jama'a tasa gudunmawar da zai bayar ba.

Alhaji Dahiru Mangal ya bayar da gudunmawar miliyan N25, iyalin Kam Salems sun bayar da gudunmawar miliyan N2.

Gwamnatin jihar Borno ta bayar da tallafin miliyan N10, a yayin da gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi ta bayar da tallafin miliyan N25 a karo na farko, tare da daukan alkawarin yin kari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Hajiya Maryam Abacha ta bayar da gudunmawar miliyan N5 amadadinta da kuma iyalanta.

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayar da gudunmawar miliyan N20, a yayin da majalisar sarkin Musulmi ta bayar da gudunmawar miliyan N5. Kazalika, wasu manyan mutane daga jihar Sokoto sun bayar da gudunmaawar miliyan N40.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel