Gwamnatin tarayya ta karrama manyan jami'an gwamnati 82

Gwamnatin tarayya ta karrama manyan jami'an gwamnati 82

Wani sakataren dindindin mai ritaya a ma'aikatar harkokin Neja Delta, Aminu Aliyu Bisalla, na daya daga cikin manyan ma'aikatan gwamnatin tarayya 82 da aka karrama a sanadiyar kwazon aiki kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mukaddashiyar shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan, ita ta karrama manyan jami'an gwamnatin tare da antaya masu lambar yabo yayin wata liyafar dare da aka shirya dangane da wannan babban taro yayin kawo karshen bikin makon ma'aikatan gwamnati.

A yayin taron da aka gudanar a karshen makon da muke da ciki a babban dakin taro da ke fadar shugaban kasa ta Villa a garin Abuja, Dr. Folasade ta ce wadanda aka karrama sun samu wannan lambar girma a sanadiyar kwazo, kwarewa, jajircewa, da kuma sadaukar da kai da suka yi yayin sauke nauye-nauyen yi wa kasa hidima da ya rataya a wuyansu.

A cewar ta, wannan lambar yabo na zuwa ne kai tsaye daga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin karrama manyan ma'aikatan gwamnati ka ma daga matakin sakatarorin dindindin zuwa ga daraktocin ma'aikatu da sauransu.

KARANTA KUMA: Alhaji Baba Abba Yusuf: Kwamishinan hukumar INEC na jihar Taraba ya riga mu gidan gaskiya

Ta kara da cewa, wannan karamci yayi daidai da akidar gwamnatin Buhari da kuma tsare-tsarenta na habaka jin dadin ma'aikata domin kara masu karsashi na inganta kwazon aiki.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel