Alhaji Baba Abba Yusuf: Kwamishinan hukumar INEC na jihar Taraba ya riga mu gidan gaskiya
- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta sanar da mutuwar kwamishinanta na jihar Taraba, Alhaji Baba Ahmed Yusuf.
- Sakatariyar hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ita ce ta bayar da sanarwa a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumba.
- Alhaji Yusuf ya riga mu gidan gaskiya a asibitin koyar wa na jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno a ranar Asabar, 28 ga watan Satumba
- Mrs Rose ta misalta marigayi Alhaji Baba wanda aka nada kwamishinan INEC a shekarar 2010, a matsayin mutum mai tsayuwa bisa gaskiya kuma daya daga cikin kwararrun ma'aikatan hukumar
Mun samu cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta sanar da mutuwar Alhaji Baba Abba Yusuf, kwamishinta na reshen jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Kamar yadda sakatariyar hukumar Mrs Rose Oriaran-Anthony ta sanar, ajali ya katse hanzarin marigayi Yusuf a ranar Asabar, 28 ga watan Satumba, a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri ta jihar Borno.
Mrs Anthony yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Nation a ranar Lahadi, 29 ga watan Satumban 2019, ta misalta marigayi Alhaji Baba a matsayin mutum mai tsayuwa bisa gaskiya kuma daya daga cikin kwararrun ma'aikata na hukumar.
KARANTA KUMA: Manyan Limamai 7 da suka yi da'awar samun wahayi daga wurin Ubangiji
Legit.ng ta fahimci cewa, an gudanar da jana'izar marigayi Alhaji Baba a ranar Lahadin yau a bisa tsari na addinin Islama kamar yadda Mrs Anthony ta labarta.
A yayin tabbatar da babban rashin da suka yi da maye gurbinsa zai yi matukar wahala, Mrs Anthony ta ce marigayi Alhaji Baba wanda hukumar INEC ta nada mukamin kwamishina tun a shekarar 2010, ya yi aiki a wannan mukami a jihohin Benuwe da kuma Adamawa gabanin jihar Taraba.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng