Manyan Limamai 7 da suka yi da'awar samun wahayi daga wurin Ubangiji

Manyan Limamai 7 da suka yi da'awar samun wahayi daga wurin Ubangiji

A cikin 'yan ritsin nan da muke ciki da kuma lokutan da suka shude a baya, an samu wasu manyan limaman addinin kirista da suka yi da'awar annabta kuma suka sha mugunyar kunya sanadiyar karairayi da suka shirga a kasar nan.

Babu shakka wasu fitattun limamai na addinin kirista da dama sun yi da'awar annabta da cewar an yi masu wahayin wasu ababen da za su faru a kasar nan da kuma wajen Najeriya, sai dai kuwa ga shi lokutan ababen na da'awa da suka yi ya zo ya shude ba tare da sun tabbata ba.

Jaridar PM News a rahoton da ta wallafa a ranar 28 ga watan Satumba, ta jeranto wasu manyan Limamai na addinin kirista da suka shirga karya ta da'awar annabta da sanin gaibu. Ga jerin su kamar haka:

1. Rabaran Chris Okotie

Okotie wanda ya kasance babban limamin cocin Household of God Church dake birnin Ikeja na jihar Legas, yayi da'awar shi zai lashe zaben shugaban kasa na 2003 a yayin da ya fito takara a karkashin inuwa ta jam'iyyar Justice Party.

Babu shakka Okotie ya sha kunyar gaske a yayin da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya lallasa wajen lashe zaben kasa na 2003.

Makamanciyar hakan ta sake kasancewa biyo bayan da'awar annabta, inda Rabaran Okotie ya sake shan mugunyar kunya yayin da tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua ya hambarar da shi a zaben kasa na 2007.

Da yake dai kunya ba ta da wurin zama a ido ko kuma zuciyar Rabaran Okotie, a shekarar 2014 ya sake da'awar cewa Ubangiji ya umarce shi da sake fitowa takarar shugabanci Najeriya karo na uku, lamarin da ya zuwa labari ya sha bam-ban yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa'adin sa na farko kuma yanzu yana kan ganiyar na biyu.

2. T. B Joshua

Babban mai da'awar annabtar nan kuma shugaban masana gaibu na SCOAN, The Synagogue Church of All Nations, Prophet T. B Joshua, a watan Nuwamban 2016 ya shaidawa duniya cewa, mace ce za ta lashe zaben shugaban kasar Amurka na wancan lokaci inda yake nufin Hillary Clinton, wadda shugaban kasar Donald Trump yayi nasara a kanta. Sai dai da ya ke kunya ba ta ishe sa ba, Joshua ya ce addu'o'in al'ummar Amurka ne suka yi tasiri wajen sauya sakamakon zaben.

3. Fasto Tunde Bakare

Mutane da dama ba za su manta da Fasto Bakare ba, wanda ya kasance babban Fasto na Latter Rain Assembly, inda yayi da'awar ilimin gaibu da cewar mutuwa za ta cimma Cif Olusegun Obasanjo gabanin a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 1999.

Ya zuwa yanzu bayan shafe tsawon shekaru takwas na wa'adi biyu a kan karagar mulki, tsohon shugaban kasa Obasanjo na nan da rai cikin koshin lafiya.

4. Johnson Suleman

Ana iya tuna cewa Johson Suleman wanda ya kasance babban limamin Omega Fire Ministry, ya jinginawa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i mutuwa muddin bai janye dokar da'awar da ya shimfida a jiharsa ba. Har yanzu wannan doka tana nan kuma gwamna El-Rufa'i na nan da ransa.

Hakazalika Johnson Suleman ya ce muddin al'ummar kasar Amurka ba su dukufa ba wajen kwarara addu'o'i, ta babu makawa tsohon shugaban kasar Barack Obama, zai nemi ya jagoranci kasar a wa'adi na uku kuma babu lallai ayi zabe a kasar. Sai kuwa ga shi wannan lamari bai tabbata ba.

KARANTA KUMA: Abin da yasa ake takun saka tsakanin Saudiya da Iran

5. Fasto Samuel Akinbodunse

Gabanin babban zaben kasa na 2019, Fatsto Samuel Akinbodunse, wani babban limamin addinin kirista na Najeriya mazauni a kasar Afirka ta Kudu, ya yi da'awar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi nasara ba kuma ajali zai cimma masa gabanin zaben.

A yayin da Fasto Samuel ya rinka gargadin Buhari da cewar neman takarar shugabancin Najeriya wuce gona da iri ne domin kuwa ajalinsa yake kira ba tare da ya sani ba, ya zuwa yanzu da yake karya fure take ba ta 'ya'ya, Buhari na kan ganiyar jagorantar Najeriya a wa'adi na biyu cikin karsashi da koshin lafiya.

6. Rabaran Simeon Ononogbu

Ononogbu wanda ya kasance babban fasto a jihar Ebonyi, yayi da'awar sanin gaibu yayin wata hira da manema labarai, inda ya ce kungiyar 'yan kwallon kafar Najeriya ta Mata wadda aka fi sani da Falcons, za ta je mataki na biyu kasreh a gasar kofin duniya na mata da aka fafata a bara cikin kasar Faransa, kuma mai masaukin bakin za ta gama gasar a mataki na biyar.

Wannan lamari bai tabbata ba inda Rabaran Ononogbu ya alakanta lamarin da cewa shaidan ne ya yaudare shi, sai dai a yayin da kasar Faransa tazo a mataki na biyar bayan kammala gasar, ya ce tabbas wannan wahayi ne da ya tabbatar daga Ubangiji zuwa gare shi.

7. Bishop Wale Olagunju

Babban limamin cocin Divine Seed of God Chapel Ministries dake birnin Ibadan na jihar Oyo, Wale Olagunju, ya da'awar cewa shugaban kasa Buhari zai sha kashi a hannun Atiku Abubakar a a yayin babban zaben kasa na 2019 da ya gabata.

Tun gabanin zaben Olagunju ya fara taya Atiku murna, da cewa nasararsa sai ta tabbatar domin kuwa tamkar kaddara ce da rigayi fata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel