Tirkashi: An gano makarantun kudi na bogi guda 10 a jihar Sokoto

Tirkashi: An gano makarantun kudi na bogi guda 10 a jihar Sokoto

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce ta gano wasu makarantun kudi guda 10 da aka kirkira na karya.

Mai magana da yawun ma'aikatar kula da makarantun frimari da sakandari na jihar, Nura Bello Maikwanci ne ya bayyana hakan a ranar Asabar.

A hirar da ya yi da Daily Trust, Mailkwanci ya ce makarantun sun nemi izinin yin rajista amma lokacin da aka kai ziyara a addreshin da suka bayar ba a komai ba.

"Mun gano cewa babu makarantun. Kawai duk na bogi ne kuma ba mu san dalilin da yasa suka nemi izinin yin rajistan ba," inji shi.

Makarantun dai sune; Nursery and Primary School, Shuni Road, Sokoto; Grace International School, Nakasari, Sokoto; Spring – Field International School, Unguwar Rogo, Sokoto da Alkhairi International School, Bodinga.

DUBA WANNAN: Harin da aka kaiwa Pantami: 'Yan sanda sun gayyaci jiga-jigan PDP 3 don amsa tambayoyi

Sauran sun hada da TAC Academy Kwannawa, Sokoto; Rhema International School, Kwannawa; Kids Ambassadors Nakasari Area, Sokoto; the Sokoto Academy, Mana, Sokoto; De – Trend Day Care School, Old Airport, Sokoto and International Academy for Excellence, Badon Barade, Sokoto.

Nura ya kuma ce an rufe wasu makarantun kudi uku a jihar saboda rashin kyawun muhalli.

Makarantun da aka rufe sune; Coral Foundation Spring Montessori, Sokoto, Brighter Children School, Koko Road, Sokoto da Godiya Nursery and Primary School, Tambuwal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel