Tarihin kadan daga cikin jaruman Kannywood masu tasowa

Tarihin kadan daga cikin jaruman Kannywood masu tasowa

- Masana'antar Kannywood na daya daga cikin masana'antun fina-finai da ke habaka da gaggawa

- Zamu iya danganta hakan da cikakkiyar al'adar malam bahaushe da jaruman ke bayyanawa

- Kadan daga cikin jaruman masana'antar sun hada da Maryam Yahaya, Umar M. Sharif, Garzali Miko da sauransu

Masana'antar Kannywood na daga cikin masana'antun fina-finai a Najeriya masu habaka.

Sigar da masana'antar ke habaka za a iya dangantata da cikakkiyar al'adar malam bahaushe da ake nunawa a fina-finan.

Sama da shekaru 20 da samuwar masana'antar, ta kasance babbar hanyar samar da aiyuka ga matasa masu hazaka a arewacin kasar nan.

KU KARANTA: Bukatar-rinjaye-ce-ta-sa-nake-kashe-mutane-ji-shugaban-kungiyar-masu-garkuwa-da-mutane

Ga kadan daga cikin matasa masu tasowa a masana'antar.

1. Maryam Yahaya: Tana daya daga cikin matasan yam mata da a halin yanzu ke tashe a masana'antar. Tauraruwarta ta fara haskawa ne tun bayan da ta yi shirin fim mai suna Mansoor. Fim din da yai matukar kayatar da masu kallo wanda jarumi Ali Nuhu ya bada Umarni.

An haifi jarumar ne a Goron Dutse a cikin jihar Kano. Ta yi makarantar firamare a Yelwa kafin ta yi karatun sakandiren ta a barikin Bokabo inda daga baya ta fada harkar fim don cika tsohon burinta.

2. Maryam Booth: Duk da Maryam ta dade a masana'antar Kannywood, iya sajewa da duk abinda aka sanyata yasa ta zamo tauraruwa a fina-finan hausa a fadin kasar nan.

Diyar daga cikin tsoffin jaruman masana'antar, Maryam Booth, ta fara shirin fim ne tun tana da shekaru 8 a duniya. Ta yi suna ne tun bayan da ta fito a fim din Dijangala a 2007.

An haifi Maryam Booth ne a ranar 28 ga watan Oktoba, 1993. Ta yi karatun firamarenta a makarantar Ebony inda ta kammala na sakandire a Ahmadiya.

Ta hidimtawa kasarta bayan da ta kammala digirinta.

3. Umar M. Sharif: Matashin mai shekaru 31 an san shi ne da baiwar waka kafin a fara haskasa a fina-finan hausa.

An haifeshi a garin Kaduna. Jarumin ya yi fina-finai irinsu Mahaifiyata, Nas, Jinin Jikina, Bazan barki ba da sauransu. Babu shakka Sharif na daga cikin matasan da ake yayi a halin yanzu a masana'antar.

4. Garzali Miko: Tsohon darakta wanda a yanzu ya koma fitowa fina-finai. Miko na hannun daman Sarki Ali Nuhu ne. Ya fito haske ne bayan rawar da ya taka a fim din da Ali Nuhu ya bada Umarni na gamu nan dai.

Kwarewarshi a maida rubtaccen lamari zuwa shirin fim yasa ya zamo abin so ga mutane. Miko ya bayyana a fina-finai kamar su Hadari, Ameerah, Zee Zee, Guguwar so, Makaryaci da sauransu.

Sauran jaruman Kannywood masu tasowa sun hada da: Jaruma Hassana Muhammad, Jaruma Aishatul Humaira, Jaruma Amal Shu'aibu, Jaruma Bilkisu Shema, Jaruma Bilkisu Abdullahi da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel