Bukatar rinjaye ce ta sa nake kashe mutane, in ji shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane

Bukatar rinjaye ce ta sa nake kashe mutane, in ji shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane

- Hukumar 'yan sandan jihar Benue sun kara binciko wasu kaburbura a karamar hukumar Ushongo na jihar

- Masu garkuwa da mutane da fashi da makamin da ke addabar yankin ne ke birne mutanen da suka kashe

- Shugaban kungiyar ya ce bukatar rinjaye ce ta kashe mutane kuma aljana sarauniya ce ta umarcesa da birnesu

A jiya hukumar 'yan sandan jihar Benue suka cafke shugaban masu garkuwa da mutane da suka kware a kashe mutane tare da birnesu.

'Yan sandan sun bayyana cewa an kama mutane 40 da suke da hannu a fashi da makami da garkuwa da mutane.

An samu miyagun makamai a wajensu sannan ana bincikarsu da garkuwa da mutane da fashi.

Kwamishinan jihar Benue, Mukaddas Garba, ya yi magana akan cigaban. Ya ce an kama shugaban kungiyar, Iorwuese Ikpila da wasu mutane 5 a Gbaste Ushongo lokacin da 'yan sanda suka samu bayani game da kungiyar.

KU KARANTA: Jirgin-kwantar-da-tarzoma-ya-yi-hatsari-a-jamhuriya-afirka-ta-tsakiya

Kamar yadda ya sanar, "Mun samo bayanan sirri akan garkuwa da mutane da fashi da makami da ke faruwa a karamar hukumar Ushongo ta jihar Benue,"

Ya kara da cewa, "Bayan samuwar bayanan, mun tura jami'an tsaro yankin son bincike. A ranar 21 ga watan Satumba, 2019 wajen large 4:30 jami'an tsaro suka kama shugaban kungiyar da wasu mutane 5,"

"A yayin bincikarsu ne aka gano cewa sune 'yan fashin da ke addabar kananan hukumomin Zone A, Ukum, Kwande, Katsina-Ala da Ushongo na jihar." In ji kwamishinan.

Kamar yadda ya fada, cigaban bincike ya sa aka gano wasu kaburbura 16. An kuma kama mai sayen kayayyakin da barayin suke kwacewa mutane."

A zantawa da manema labarai da shugaban kungiyar ya yi, ya ce ya fara harkar garkuwa da mutane ne tun watanni uku da suka gabata.

Ya kara da cewa, shi da 'yan kungiyarsa na shake mutanen da suka kama ne har lahira.

Ya ce bukatar babban rinjaye ne yasa yake kashe mutane. "Aljana sarauniya ce ta bani umarnin yadda zan dinga birne mutane."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel