Wa'iyazubillah: An kama uba dumu-dumu yana zina da diyarshi ta cikinsa

Wa'iyazubillah: An kama uba dumu-dumu yana zina da diyarshi ta cikinsa

- An kama wani mutumi mai suna Yesiru Onajobi da laifin yiwa 'yarshi fyade

- Mutumin wanda yake manomi ne an kama shi ya haikewa 'yarshi mai shekaru goma sha hudu

- Alkalin kotun da aka gurfanar da shi a gaban shi ya yanke masa hukuncin shekara goma a gidan kaso babu beli

An yankewa wani manomi a jihar Legas mai suna Yesiru Onajobi hukuncin shekara 10 a gidan yari, bayan an kama shi da laifin yiwa 'yarshi mai shekaru goma sha hudu fyade.

Alkalin babbar kotun dake jihar Legas mai shari'a Sule Hassan, ya yankewa Onajobi hukuncin shekara goma a gidan yari, bayan an kama shi da laifin fyade da keta haddin 'yar tashi.

"Na saurari korafin kowanne bangare, duk da dai bangaren wanda ake kara bai bada wata hujja kwakkwara ba.

KU KARANTA: Babbar magana: Ni ciwon da nake yi na satar jarirai ne - In ji matar da aka kama da jariri

"Laifin da ake tuhumar sa dashi babban laifi ne, saboda haka na yanke maka hukuncin shekara shekara goma a gidan kurkuku ba tare da beli ba ko tara.

"Haka kuma lokacin da ka dauka ana tsare da kai a ofishin 'yan sanda za a cire shi a cikin shekarun da zaka yi," in ji alkalin kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel