Jirgin kwantar da tarzoma ya yi hatsari a Jamhuriya Afirka ta tsakiya

Jirgin kwantar da tarzoma ya yi hatsari a Jamhuriya Afirka ta tsakiya

- A ranar juma'a ne jirgin kwantar da tarzoma na kasar Senegal ya yi hatsari a jamhuriyar Afirka ta tsakiya

- Mankeur Ndiaye, shugaban MINUSCA ne ya wallafa hakan a shafinsa na tuwita

- Hatsarin ya auku ne yayin da jirgin ke sauka a wani birni na yammacin Bouar

Abin alhini ya auku a ranar juma'a a jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Jirgin kwantar da tarzoma na majalisar dinkin duniya ya yi hatsari inda aka tabbatar da cewa mutane 3 sun rasa rayukansu.

Daraktan yada labarai da hulda da jama'a na sojin kasar Senegal, Col. Abdoul Ndiaye ya ce jirgin na sojin saman kasar ne wanda aka tura MINUSCA kuma yana dawowa ne daga aikin da aka turasa.

KU KARANTA: Mahaifinta-ya-sanya-ta-a-mari-tare-da-garkameta-na-shekaru-2-saboda-auren-dole

Shugaban MINUSCA, Mankeur Ndiayeh ya bayyana cewa hatsarin jirgin saman ya faru ne yayin da jirgin ke sauka a wani birni na yammacin Bouar. Hakan ne kuwa ya kawo sanadiyyar rasa mutane 3 inda mutum daya ya samu rauni.

"Da tsananin damuwa nake sanar da hatsarin jirgin yaki na Senegal a yayin da yake sauka a Bouar. Hakan ya yi sanadin mutuwar mutane 3 da raunata mutum daya," Mankeur Ndiaye ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Idan zamu tuna, kasa Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na cike da tarzoma bayan musulmai 'yan tawaye sun yi juyin mulki ga gwamnatin shugaban kasa Francois Bozize a 2013.

Hantsilar da gwamnatin ta karfi da yaji ne ya kawo maida martanin da 'yan tawaye mabiya addinin kirista ke yi a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel