Bukatar komawa gidan yari ta sa na kara sata, in ji wani barawo

Bukatar komawa gidan yari ta sa na kara sata, in ji wani barawo

- Wani mutum mai shekaru 39 da ake zargi da satar babur ya bayyanawa jami'an tsaro cewa burin komawa gidan yari yasa ya yi sata

- Barawon wanda sa'o'i biyu kacal da fitowarsa daga gidan maza, ya ce bashi da kudi, abinci ko abokai a cikin gari

- Ya bayyana cewa gidan yarin ya fi mishi saboda babu tsananin rayuwaDalilin da yasa jami'ar Bayero da ke Kano ta kori dalibai 63 tare da dakatar da 13 na shekara daya

Wani dan gidan fursuna ya kara aikata laifi sa'o'i bayan ya fito daga gidan maza. Laifin kuwa yasa aka maidasa gidan da ake bashi ci da sha kyauta, wajen kwanciya kyauta kuma manyan abokansa na jiran isarsa.

Tsohon dan gidan fursunan ya kara aikata laifi ne a yankin Chon Buri jim kadan da ya fito daga gidan gyaran hali.

KU KARANTA: Abun-kunya-saurayi-ya-yi-satar-wayoyi-da-jaka-a-gidan-sirikai

'Yan sanda sun ce an kara kama Khanchit Sutthipichai ne yayin da yake yunkurin satar babu da mota, a don haka ne ake zarginsa da sata.

Mutumin mai shekaru 39, ya sanar da 'yan sandan yankin Na Chom Tien cewa sa'o'i biyu kenan da ya fito daga gidan yari na Nong Pla Lai inda ya yi watanni 6 sakamakon kamasa da aka yi da miyagun kwayoyi.

"Bansan me zanyi ba bayan an sakeni. Banda kudi, banda abincin da zanci kuma nayi kewar abokaina da ke gidan fursuna," in ji shi.

Wanda ake zargin ya kara da cewa, "Don haka ne na saci babur yadda za a kamani kuma a maida ni gidan maza."

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, ya ce, rayuwar gidan yari ta fi mishi saboda babu wahalar rayuwa.

Ya ce, yana da abokai, abinci da wajen kwana kyauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel