Ke duniya! Yaro mai shekaru 7 a duniya da fashi da makami

Ke duniya! Yaro mai shekaru 7 a duniya da fashi da makami

- Hukumar 'yan sandan Ipswich Suffolk na neman wasu yara biyu ido rufe

- Ana zargin yaran da tsare wata mata mai shekaru 60 da wuka da bukatarsu na karbar motarta

- Daga baya an ga motar a yashe inda 'yan sanda ke neman yaran da suka yi aika-aikar

Yara biyu, daya mai shekaru 7, dayan mai shekaru 12 sunyi barazanar kashe wata mata mai shekaru 60 a yunkurinsu na kwace motarta, kamar yadda jaridar mail online ta ruwaito.

A halin yanzu 'yan sanda ma neman yaran ido rufe sakamakon aika-aikarsu.

Karamin ya bude kofar motar matar yayin da take ribas a kan hanyar Ipswich dake garin Suffolk a ranar asabar da ta gabata.

KU KARANTA: Kotu-ta-yankewa-tsohon-shugaban-nba-shekaru-3-a-gidan-gyaran-hali

Sun nunawa matar wukar tare da barazanar zasu kasheta matukar bata fice ta basu motarta ba.

A tsorace ta fice daga motar inda babban ya shiga mazaunin direba ya tada motar tare da tserewa shi da karamin da wajen karfe 6:15 na yammacin ranar asabar.

Daga baya an tsinci motar inda 'yan sanda ke nan yaran ido rufe.

A kwanakin baya jaridar nan ta ruwaito cewa an kama yaro mai shekaru 11 a cikin 'yan fashi fa bata garin da ke zama a kasan gadar Legas.

Bayan tuhumarsa da jami'an tsaro suka yi, sai ya bayyana musu cewa shi bai ga aibun shaye-shaye ba don tun yana da shekaru 9 a duniya ya fara.

Hakazalika yaron yana saida miyagun kwayoyi wadanda ya ce ogansa ne yake bashi yana siyarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel