An kuma: Wata mata ta sake tona asirin wani dan majalisa da yake lalata da ita

An kuma: Wata mata ta sake tona asirin wani dan majalisa da yake lalata da ita

- Wata mata ta sake tonawa wani dan majalisa a jihar Imo asiri

- Matar ta bayyana yadda suka shafe sama da shekara goma suna soyayya da shi har yayi mata ciki

- Ta bayyana irin alkawuran da dan majalisar yayi mata da kuma irin abubuwan da zai siya mata wadanda duka bai cika ba

Wata mata mai suna Nkeiruka Cynthia Kamalu, ta bayyana yadda dan majalisa, Uju Kingsley Chima ya kwanta da ita a shekarar 2015.

Chima dai dan majalisa ne na tarayya mai wakiltar Ohaji/Egbema, Oguta da Oru ta yamma dake cikin jihar Imo.

"Mun yi soyayya ta tsawon shekara goma, daga nan sai ya bayyana mini cewa yana so ya aure ni, duka muka amince da zama mata da miji.

"Kwatsam sai iyayen mu suka sanya baki a maganar auren mu suka bayyana cewa ai muna da dangantaka, saboda haka ba za mu iya aurar juna ba, hakan ya saka na auri wani mutumi mai suna Gabriel Igbibi.

"Chima yayi mini alkawarin ba zai taba iya rabuwa dani ba, kuma zai cigaba da kula dani yadda ya kamata. Mijina ya samu labarin dangantakar dake tsakani na da Chima, hakan ya saka yayi mini barazanar zai sake ni.

"Chima yayi mini alkawarin idan har na samu ya sake ni, zai dinga bani naira miliyan ashirin a kowanne wata shida, sannan yace zai siya mini gida a duk inda nake so a jihar Legas.

KU KARANTA: Tirkashi: Jam'iyyar PDP ta bukaci mataimakin shugaban kasa Osinbajo yayi murabus

"Haka na takura kotu ta raba auren mu da mijina, bayan rabuwar mu Chima ya bayyana mini cewa kafin ya dauki soyayyar mu da gaske sai na fara daukar ciki dashi tukunna.

"Haka kuwa aka yi na dauki ciki, amma kuma sai cikin ya zube. Sai ya ce mini yana so mu dauki dan riko shi kuma zai bayyana cewa dan shine dana haifa masa a kasar Canada, shima yaron da muka dauka din ya zo mutu, na yi masa alkawari bazan taba cin amanarsa ba, amma kawai sai gashi na kama shi da wata macen suna lalata.

"Abin ya bata mini rai sosai, shima kuma ya nuna fushin shi sosai, har yayi mini gargadin kada na kara zuwa inda yake, ya ce yanzu baya sona kwata-kwata. Na tuna mishi alkawarin da yace na dauka mishi na cewa babu wanda zai kara kwanciya dani idan ba shi ba, sannan kuma na tuna mishi alkawarin da yayi mini na bani miliyan ashirin kowanne wata shida, gida da mota wadanda duka bai cika ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel