An kama wani mutum mai damfara da sunan manajan sashin kudi na NNPC
- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da wani sojan gona da ta kama a garin Kaduna
- Dan damfarar na amfani da sunan babban manajan bangaren kudi na matatar man fetur ta Najeriya
- Ya karbi kudi N65,150,000 da zummar zai samar masa da kayayyakin man fetur da zasu kai 2,000mt zuwa 2,5000mt
Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da wani mutum mai suna Nuhu Ibrahim Shu'aibu wanda aka fi sani da Ishaku Abdulrazaq akan damfara da sunan babban manajan kudi na matatar man fetur ta kasa, NNPC.
An gurfanar da Shu'aibu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, a gaban mai shari'a P. Mallong na babbar kotun tarayya, da laifin sojan gona da kuma damfarar kudi har N65,150,000 kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
Shu'aibu ya fara damfarar ne tun 2017, a lokacin da ya gabatar da kansa a matsayin babban daraktan kudi na NNPC ga wani dan kasuwa, Malam Faisal Safiyanu, wanda ya yi wa alkawarin hanyar samun 2,000mt zuwa 2,500mt na kayayyakin man fetur.
Daga lokacin zuwa yanzu da ya shigo hannu, ya karba N65,150,000 daga wanda yake damfarar amma kayan sunki fitowa.
KU KARANTA: Adam-zango-ya-rantse-da-al-qurani-don-musanta-zargin-da-wani-malami-ya-yi-masa
An karanto laifukansa a gaban kotun kamar haka: "Cewa kai Nuhu Ibrahim Shu'aibu wanda aka fi sani da Ishaku Abdulrazaq mazaunin No 1, Khaleesa close, Millenium city Kaduna, tsakani watan Nuwamba na 2017 zuwa Mayu 2018, ka karba N65,150,000 daga Faisal Safiyanu,"
" Da zummar cewa zaka samar masa da kayayyakin man fetur wanda kasan karya ne. laifinka ya ci karo da sashi na 1 karkashin dokokin laifukan damfarar kudi da sauran laifuka na 2006 kuma abin hukuntawa ne a karkashin sashi na 1, sakin layi na 3 na dokokin."
Wanda ake karar ya musanta laifinsa wanda hakan yasa lauyan mai kara, M. Lawal da rokon koyun ta tsare wanda akai karar har zuwa lokacin da za a kara komawa kotun don cigaba da shari'ar.
Lauyan wanda aka yi kara, Sule Shu'aibu, ya roki alkalin da ya bada belin Shu'aibu don bashi damar shiryawa kafin zuwan ranar shari'ar ta gaba. Bukatar da kotun kuwa taki yarda da ita.
Mai shari'a P. Mallong ya bada umarnin a ajiye wanda ake zargin a gidan maza har zuwa ranar 30 ga watan Satumba inda za a cigaba da sauraron shari'ar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng