Wata kungiya ta koka bayan 'yan sanda sun rufe mata masallacin Juma'a a Sokoto

Wata kungiya ta koka bayan 'yan sanda sun rufe mata masallacin Juma'a a Sokoto

Wata kungiyar addinin musulunci, Islahiddini Foundation of Nigeria, ta koka kan rufe mata masallacin Juma'a da sauran masallatai a kauyen Butuku a karamar hukumar Bodinga na jihar Sokoto.

A jawabin da ya yi yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Alhamis a Sokoto, shugaban kungiyar na kasa, Uztaz Umar Liman ya ce 'yan sanda sun rufe masallacin nasu ne ba tare da wani bayani ba.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Liman ya ce an bi dukkan dokoki da ka'idoji daga hukumomin da lamarin ya shafa yayin ginin masallacin da kaddamar da shi.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe wani gawurtaccen dan fashi da ake nema ruwa a jallo

Ya ce 'yan kungiyar sun tuntubi sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar amma ya ce musu bai da masaniya kan abinda 'yan sandan suka aikata.

Ya yi bayanin cewa kungiyar sun aike da wasikun koke a ofishin mataimakin sufeta janar na 'yan sanda na yankin da kuma ofishin 'yan sandan farar hula DSS na jihar Sokoto.

Liman ya kara da cewa sun aike da irin wannan wasikun koken zuwa ga hukumar tsaro ta NSCDC da kungiyar kare hakkin bil adama (NHRC).

Ya ce rufe masallacin tauye musu hakkinsu na yin addinsu ne da dokar kasa ta basu duba da cewa ba su tayar da hankulan al'umma.

Ya yi kira ga Gwamna Aminu Tambuwal da Sufeta janar na 'yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu su saka baki a lamarin domin musulmi mutane ne masu son zaman lafiya.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun 'yan sandan jihar Sokoto, Muhammad Sadiq ya ce bashi da masaniya kan rufe masallacin.

Sadiq ya yi alkawarin yin bincike kan batun sannan zai fitar da sanarwa daga bisani.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta kuma ruwaiti cewa shugaban NHRC na jihar, Hamza Liman ya tabbatar da cewa ya samu wasikar koken kuma yana aiki a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel