Miji na yana neman yin asiri da ni: Matar aure da fadawa kotu

Miji na yana neman yin asiri da ni: Matar aure da fadawa kotu

Wata 'yan sanda mai mukamin saja, Wuraola Babaola ta shigar da mijinta kara a wani kotu da ke zamansa a Ibadan inda take neman a raba aurenta da mijinta Oladimeji kan zargin cewa ya yi yunkurin yin asiri da ita.

Acewar mai shigar da karar, Oladimeji ya kanyi amfani da layyu iri daban-daban duk lokacin da za suyi kwanciyar aure.

Ta kuma yi ikirarin cewa Oladimeji yana lakada mata duka kamar jaka.

"Da zarar abu kadan ya faru ya kan doke ni kuma ya hana 'yan uwa na gani na.

"Ya kan sa magunguna a farji na duk lokacin da zai sadu dani. Ya kan zuba layyu ya zagaye kwanon abinci na da sunan cewa yana kare ni ne.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa da mutane sun sace mataimakin shugaban karamar hukuma a Katsina

"Ya kuma binne layyu da dama a gidan mu kuma ya kan yawan ihun suna na. Dan mu na fari ya ga lokacin da ya ke aikata hakan.

"Ina da shaida a kan dukkan layun da ya ke amfani da shi da kuma yadda ya ke duka na a cikin waya na," inji ta.

Oladimeji bai hallarci kotun ba domin ya kare kansa.

Bayan sauraron koken wanda ta shigar da karar, Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade ya raba auren kan barazana ga rayuwa.

Ya bawa wanda ta shigar da karar izinin rike yaransu uku kuma ya bukaci wanda aka yi kararsa ya rika biyan N15,000 a duk wata domin kulawa da yaran.

Kotun ta bukaci a aike wa Oladimeji kofin hukuncin da kotun ta yanke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel