Aikin ‘yan sanda:PSC ta dakatar da shirin karin mukamai da kuma daukar kuratan ‘yan sanda 10,000

Aikin ‘yan sanda:PSC ta dakatar da shirin karin mukamai da kuma daukar kuratan ‘yan sanda 10,000

Hukumar da take sanya ido a kan al’amuran ‘yan sandan Najeriya wato Police Service Commission (PSC) ta dakatar da shirin daukan sabbin jami’an ‘yan sanda su 10,000.

Wannan abu ya faru ne a sakamakon rashin jituwa dake tsakanin hukumar da Sufeto janar Mohammed Adamu. An kuma cinma wannan matsayar ne a ranar Talata da hukumar ta gana da kungiyar ‘yan kwadago a Abuja.

KU KARANTA:Rashin ingantaccen jagoranci ne dalilin da ya hana Najeriya cigaba – Shugaban NUC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kungiyar ‘yan kwadagon ta shawarci hukumar PSC da tayi amfani da hanyoyin shari’a domin bincike kwamitin gudanarwar ‘yan sanda,

An dade ana kai ruwa rana tsakanin hukumar da rundunar ‘yan sandan Najeriya game da daukan kurata 10,000 inda Sufeto janar ke ganin yana da ikon daukansu.

Har ila yau, Adamu yayi watsi da maganar hukumar na cewa ta dakatar da shirin daukan kuratan inda ya fitar da sunayen wadanda suka yi nasara a tantancewar da aka yi.

Sai dai kuma hukumar PSC ta ce wannan jerin sunayen da rundunar ‘yan sanda ta fitar ba sahihi bane saboda da dama daga cikinsu ba su halarci tantancewa ba kamar yadda tsarin daukan aikin ya tanadar.

Biyo bayan rashin jituwar bangarorin biyu Shugaba Buhari ya shawarce su da su sasanta kansu. Amma sai dai wata majiya mai karfi da samu halartar ganawar kunyiyar kwadago da hukumar PSC ta sanar damu cewa za a dakatar da daukan kuratan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel