Rufe layukan waya zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a Najeriya - Pantami

Rufe layukan waya zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a Najeriya - Pantami

Ministan sadarwa na Najeriya, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya alakanta gibin da aka samu wajen rajistar layukan waya barkatar ba tare da ka'ida ba da tabarbarewar tsaro a Najeriya musamman ta'addancin masu garkuwa.

Jaridar BBC Hausa ta ambato ministan yana cewa, ci gaba da yaduwar miyagun laifuka na ta'addanci musamman ta'adar garkuwa na da nasaba mai girman gaske dangane da kuskuren da aka samu a bangaren sadarwa.

Dakta Pantami ya ce kimanin kaso 90 na miyagun laifuka da ake tafkawa a kasar na aukuwa ne da mafi girman taimako na wayoyin hannu musamman ta'adar masu garkuwa da mutane da ta addabi kasar.

A sanadiyar haka ministan ya ce ma'aikatarsa ta sadarwa za ta jajirce wajen tallafa wa hukumomin tsaro wajen dakusar da kaifin aukuwar miyagun laifuka ta hanyar rufe dukkanin layukan waya marasa rajista.

Ministan wanda kuma ya kasance babban shehin malamin addinin Islama da ya shahara a kan aikin da'awa da tafsirin Al-Qur'ani, ya ce tilas ne kowane mai amfan da wayar salula a Najeriya ya yiwa layin sa rajista domin ci gaba da ribatar duk wata harkalla ta sadarwa.

KARANTA KUMA: Har yanzu Kemi Adeosun ce ministar kudi a shafin yanar gizo na gwamnatin Najeriya

Ya ce ya zuwa yanzu a yayin da akwai layuka waya sama da miliyan 9 marasa rajista, an rufe layuka fiye da miliyan 6.7 a sanadiyar rashin sanin ainihin masu amfani da su, lamarin da ya ce hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa.

Ana iya tuna cewa, gwamnatin tarayya a ranar Litinin 16 ga watan Satumba, ta ba hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta kasa NCC wa’adin ranar 25 ga watan Satumba, domin ta toshe duk wasu layukan waya marasa rijista.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel