Soja ya kashe kanshi bayan ya shiga gida ya iske matarshi da yake so fiye da kowa a duniya kwance da gardi a gado

Soja ya kashe kanshi bayan ya shiga gida ya iske matarshi da yake so fiye da kowa a duniya kwance da gardi a gado

- Duniya babu adalci, saboda wasu abubuwa da suke faruwa masu yawan gaske

- Wata mata ta ci amanar mijinta bayan ya kwashe shekaru yana wahalar nema mata hanyar da za ta bishi Turai

- Bayan kawo ta da shekara biyu mutumin ya shiga gida ya iske ta kwance da wani katon gardi suna lalata akan gadon su

An ruwaito cewa wani mutumi dan shekara 29 mai suna Prince Yeboah Wiredu, ya kashe kanshi bayan matar shi da yake so fiye da komai da kowa a duniya ta raina masa hankali ta mayarr da shi wawa.

A yadda rahoton ya ruwaito, mutumin wanda yake jami'in soja ne ya kama matar tashi kwance da wani katon gardi a gado, bayan ya gama wahalar nema mata wajen zama a kasar Amurka daga Ghana.

Faston da mutumin yake zuwa cocin shi ibada ya bayyana hakan a kafar sada zumunta, in da yace sojan ya mutu ne a satin da ya gabata ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2019.

KU KARANTA: Iko sai Allah: A karon farko 'yan Najeriya bakaken fata sun haifi jaririya baturiya

Ga abinda Fasto din ya rubuta:

"Ya kawo matarshi kasar Amurka da kyar shekara biyu da suka gabata daga kasar Ghana. Yaje aiki ya dawo gida a gajiye kawai ya iske matar shi kwance da wani katon gardi akan gadon su suna zina, shi kuma yaji ba zai iya jurewa ba kawai ya kashe kanshi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel