An dakatar da 'yan majalisar jihar Jigawa biyu na tsawon watanni shida

An dakatar da 'yan majalisar jihar Jigawa biyu na tsawon watanni shida

Majalisar Jihar Jigawa, a ranar Talata ta dakatar da wasu manyan jami'anta biyu na tsawon watanni shida kan yunkurin da su kayi na dakile wata bincike da majalisar ke gudanarwa.

Wadanda aka dakatar sun hada da tsohon bulaliyar majalisa, Aminu Sale Sankara ( Ringim) da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar Mista Sani Isiya (Gumel) dukkansu 'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC)

Shugaban kwamitin sadarwa na majalisar, Aminu Zakari (Gwiwa) ne ya sanar da dakatarwar mamabobin biyu yayin zantawa da manema labarai bayan zaman majalisar na ranar Talata.

DUBA WANNAN: Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

Ya ce an dakatar da 'yan majalisar ne saboda yunkurin da su kayi ne dauke wasu takardu daga ma'aikatar kudi na jihar da niyyar kawo tsaiko ga bincike da majalisar ke yi kan abubuwan da suka wakana yayin wa'adin mulkinsu.

Ya ce an dakatar da 'yan majalisun biyu tsawon watanni shida kowannensu domin majalisar da samu lokacin gudanar da bincike kan irin katsalandan din da 'yan majalisar suka gudanar.

Da aka tuntube shi, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar ya musanta zargin da ake musu inda ya ce ba mutuncin dan majalisa bane a same shi da aikata irin wannan laifin.

A watan Mayun 2019 ne aka tsige Sule da Ishaq tare da tsohon kakakin majalisar, Mista Isah Idris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel