Gwamnan Borno zai baiwa mutane miliyan 2 marasa aikin yi aiki

Gwamnan Borno zai baiwa mutane miliyan 2 marasa aikin yi aiki

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bullo da wani sabon shirin samar ma dimbin matasan jahar Borno aikin yi ta hanyar amfani da kimiyya da fasahar yanar gizo, domin taimaka ma rayuwarsu.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Alaji Engr Ibrahim Ismail ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda yace gwamnan ya kaddamar da wannan shiri ne ta wani shafin yanar gizo a karkashin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta jahar Borno.

KU KARANTA: Rashin Imani: Yan bindiga sun amshe N250,000 sun kashe wanda suka sata a Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ta cikin wannan shafin ne matasan jahar Borno da duk wani mai neman aikin yi dan asalin jahar Borno zai bi ya ciccike bayanansa domin gwamnati ta duba aikin daya dace da shi kafin a daukeshi.

Ana sa ran shafin zai dauki bayanan mutane sama da miliyan 2, kamar yadda sabon kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta jahar, Dakta Babagana Mustapha ya tabbatar, inda yace manufar kirkirar shafin shi ne a samar da wata matattarar bayana a yanar gizo da za ta kunshi bayanan dukkan masu neman aiki a jahar.

Kwamishina Babagana ya kara da cewa da wannan bayanai ne za'a samar musu da ayyuka a matakin kasa, jaha da kuma kananan hukumomi, hakazalika gwamnati ka iya amfani da bayyanan wajen sama musu da ayyuka a kungiyoyi da kamfanoni masu zaman kansu.

Ga masu sha’awar cikawa domin gudun kar ta kwana tare da kokarin ribatar wannan gwaggwabar dama daga gwamnatin jahar Borno, suna iya bin adireshin shafin kamar haka; bornojobbank.com

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel