Ku nada kashi a gindi - Cewar kotu akan Shekarau, Wali, da Ahmed

Ku nada kashi a gindi - Cewar kotu akan Shekarau, Wali, da Ahmed

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta bayyana yadda ta kaya tsakaninta da Sanata Ibrahim Shekarau kan zargin almundahanar milyan 950.

EFCC ta jawabin da ta saki ta bayyana cewa kotu ta yi watsi da bukatar da Shekarau, Aminu Wali da Ahmed, suka gabatar.

Jawabin yace: "Alkali Lewis Allagoa na babban kotun tarayya dake Kano a ranar Litinin, 23 ga Satumba, 2019 ta bayyanawa tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai ci, Malam Ibrahim Shekarau, cewa ya nada kashi a gindi kan zargin almundahanan milyan 950 da ake yi masa tare da wasu biyu.

Sauran biyun sube: Aminu Bashir Wali da Mansur Ahmed. An gurfanar da su ne ranar 24 ga Mayu, 2018 kan zargin karban kudi daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madueke, domin yakin neman zaben 2015.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Ranar Laraba kotu zata raba gardama tsakanin Ganduje da Abba

Bayan gurfanar da su, Malam Shekarau da sauran biyun sun musanta zargin da ake yi musu. A ranar 2 ga Yuli,2019, su bayyanawa kotu cewa basu da wani laifi.

Daga lokacin aka dage karar zuwa ranar 23 ga Satumba, 2019 domin yanke hukunci kan hakan.

A hukuncin da aka yanke, Alkali Allagoa ya yi watsi da maganar cewa basu da laifi kuma ya ce su fito kare kansu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel