Gwamna Badaru ya kaiwa Majalisar Jigawa sunayen kwamishinoni guda 11
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru ya kaiwa Majalisar dokokin jihar Jigawa sunayen zababbun kwamishinoninsa guda 11.
Kakakin majalisar, Idris Garba Jahun ne ya bada wannan sanarwar ranar Talata 24 ga watan Satumba a farfajiyar majalisar dokokin.
KU KARANTA:Gwamnatin Kebbi za ta soma biyan sabon mafi karancin albashi a watan Satumba – SSG
Daga cikin sunayen akwai: Dr Abba Zakari, Engr. Aminu Usman, Ibrahim Garba Hannun Giwa, Ibrahim Baba Chaichai, Mohammed Alhassan, Kabiru Hassan Sugungu.
Sauran kuwa sun hada da: Babangida Umar Gantsa, Yalwa Da’u Tijjani Tati, Salish Zakar, Lawan Yunusa Danzomo da Barrister Musa Adamu Aliyu.
A wani labarin mai kama da wannan kuwa, zaku ji cewa, Gwamnan Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya bada umarnin a fara biyan ma’aikatan jihar Kebbi mafi karancin albashin N30,000 daga wannan watan na Satumba.
Sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Babale Yauri ne ya bada wannan sanarwar ranar Litinin 23 ga watan Satumba a Birnin Kebbi babban birnin jihar Kebbi.
https://www.dailytrust.com.ng/badaru-transmits-names-of-commissioner-nominees-to-jigawa-assembly.html
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng