Mata an motsa: Mata 14 ne suka lashe zaben fidda gwani a jihar Adamawa karkashin jam'iyyar APC

Mata an motsa: Mata 14 ne suka lashe zaben fidda gwani a jihar Adamawa karkashin jam'iyyar APC

- Babu kasa da mata 14 da suka lashe zaben fidda gwani a kananan hukumomin jihar Adamawa

- Mace daya ce ta lashe zaben kujerar shugabar karamar hukuma inda 13 suka samu na kansiloli

- Sakataren yada labaran jam'iyyar APC na jihar, ya ce sun shirya tsaf don zaben watan Nuwamba da ke tunkarowa duba da irin zaben fidda gwanin da ya gabata

Mata 14 ne suka lashe zaben fidda gwani a kananan hukumomin jihar Adamawa karkashin jam'iyyar APC.

Sakataren yada labarai na jihar, Alhaji Mohammed Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a garin Yola yayin da yake jawabi ga manema labarai akan zaben fidda gwanin da ya gudana a ranar Lahadi.

Abdullahi ya ce Sopia Elisha ita kadai ce macen da ta lashe zaben fidda gwanin don takarar shugabar karamar hukumar Numan. Ta fito ne ba tare da adawa ba don haka ta tabbata da kuri'u 289.

Sauran matan 13 kuma sun lashe zaben fidda gwanin ne na shuwagabannin gundumomi a fadin jihar.

Abdullahi ya ce a cikin kananan hukumomi 21 na jihar, sakamakon zaben fidda gwanin Madagali, Yola ta kudu da Toungo ne har yanzu basu fito ba.

KU KARANTA: Tirkashi: Ya kashe kansa akan ya fadi wasan Bet9ja

Abdullahi ya ce 'yan takarar kananan hukumomin Numan, Hong da Guyuk sun fito ne ba tare da adawa ba inda na Song, Shelleng, Girei, Lamirde da Fufore sun fito ne bayan da sauran abokan hamayyar suka yi musu mubaya'a.

Ya ce 'yan takarar da suka fito ta zabe kuma sun hada da kananan hukumomin Mubi ta arewa, Maiha, Ganye, Mubi ta kudu, Gombi, Yola ta arewa, Demsa da Mayo-Belwa.

"Mun samu korafi 35 na zaben fidda gwanin gundumomi da aka yi a gundumomi 226 wadanda duk mun shawo kansu. A halin yanzu bamu samu wani korafi ba daga zaben fidda gwanin kananan hukumomi," in ji Abdullahi.

A shirye-shiryen zaben watan Nuwamba kuwa, Abdullahi ya ce duba da irin zaben gaskiya da aka yi na fidda gwanin, jam'iyyar APC a shirye take.

Ya ja kunnen jama'a masu yunkurin juya zaben akan tabbas zasu fuskanci fushin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel