Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kone yaro Musulmi dan shekara 15 a Indiya saboda yaki komawa addinin Hindu

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kone yaro Musulmi dan shekara 15 a Indiya saboda yaki komawa addinin Hindu

- A kasar Indiya an sanyawa wani yaro dan shekara 15 wuta saboda yaki furta wata kalma da za ta fitar dashi daga addinin Musulunci

- An bayyana cewa wasu mutane ne guda hudu suka kama yaron inda suka nemi ya furta wannan kalmar bayan yaki furtawa suka sanya masa wuta

- Sai dai wata majiyar kuma ta bayyana cewa yaron shi da kanshi ya sanyawa kanshi wuta

Wasu mutane sun sanyawa wani yaro Musulmi wuta saboda yaki ya furta wata kalma ta addininsu na Hindu, a yankin Chandauli dake Uttar Pradesh, cikin kasar Indiya.

An bayyana cewa wasu mutane ne guda hudu suka yi garkuwa da yaron inda suka zuba mishi kalanzir suka kunna masa wuta bayan sunce ya furta wata kalma ta addinsu yaki furtawa.

Mujallar Indian Magazine ta bayyana cewa mutanen sun bar yaron cikin wani mawuyacin hali, inda kusan kashi sittin na jikinshi ya kone.

KU KARANTA: To fah: Sai sun nemi suyi zina dani kafin su sanya ni a fim - Jaruma ta tonawa masu shirya fina-finai asiri

Sai dai kuma 'yan sandan na Chandauli sun bayyana cewa yaron shine da kanshi ya sanyawa kanshi wuta, in ji jaridar India Today.

An kaiwa mutane da yawa hari a kasar Indiya bayan an tilastasu su furta kalmar "Jai Shri Ram", ma'anar ta da Hausa shine "Ya Ubangiji Rago". Wanda yake daya daga cikin abin bauta a kasar Indiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel