Ya saci doya a gonar dan sanda, kotu ta ce a daureshi tsawon wata daya a kurkuku

Ya saci doya a gonar dan sanda, kotu ta ce a daureshi tsawon wata daya a kurkuku

A ranar Juma'a, 20 ga watan Satumba, wata kotun majistare dake Minna, jihar Neja ta yankewa wani matashi mai suna Samaila Abdullahi hukuncin daurin wata daya a kurkuku kan laifin satan doya a gonar wani jami'in dan sanda.

An caji Abdullahi da laifin sata, wanda ya sabawa sashe ta 287 na dokar jihar.

Alkali mai shari'a, Binta Rijau, ya yankewa Abdullahi hukuncin ne bayan ya amsa laifin cewa lallai ya aikata laifin.

Amma Alkalin ta baiwa Abdulahi daman biyan taran N3,000.

Lauyan gwamnati, Sifeto Thomas Peter, ya bayyanawa kotu cewa an damke Samaila Abdullahi ne aranar 15 ga watan Satumba, 2019.

Peter yace Sama'ila ya sace manyan doya takwas daga gonar tsohon jami'in dan sanda Usman Yakubu )mai murabis) a Tutungo, karamar hukumar Paikoro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel