An damke budurwa mai garkuwa da mutane a jihar Gwambe

An damke budurwa mai garkuwa da mutane a jihar Gwambe

Hukumar yan sandan jihar Gombe ya ceto wani yarinya mai shekaru hudu da haihuwa, Aishatu, daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar.

Rundunar yaki da yan fashi da makamin jihar sun bayyanawa duniya masu garkuwa da mutanen wanda ya hada da wata budurwa, Hadiza Babayo, yar shekara 25 da haihuwa, da wani Bala Shu'aibu, a ranar Juma'a.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mary Malum, ya bayyana cewa ta samu labarin leken asiri ne kan su kuma aka damke budurwar a garin Lafiya, karamar hukumar Lamorde ta jihar Adamawa.

Tace: "Yayin bincike, Hadiza Babayo, ta laburta cewa lallai ita mai garkuwa da mutane ce kuma ta bayyana yadda iya tare da Bala Shua'ibu suka sace yar makarantar Gombe High school kuma suka ajiyeta a Nayi-Nawa quarters Gombe."

Sun bukaci iyayen yar makarantar kudin fansan naira milyan shida kafin su saketa

An damke budurwa mai garkuwa da mutane a jihar Gwambe
An damke budurwa mai garkuwa da mutane a jihar Gwambe
Asali: Facebook

Hadiza ta kara da cewa ita ta gayyaci saurayinta ne domin sace diyar yayanta domin amsan kudi a hannunshi.

Tace: "Bayan dawo da ita daga makaranta, sai na shirya da saurayina (Shuaibu) domin yin amfani da damar wajen amsan kudi hannun yayana tun da baya kula da ni yadda ya kamata."

KU KARANTA: Matashi mai satan wayoyin wuta ya mutu cikin Taransfoma (Bidiyo)

Dan'uwanta, Alhaji Umar Shafudeen, wanda yayi magana da manema labarai ya bayyana irin halin da suka shiga tun ranar da akayi garkuwa da Aishatu.

Yace: "Mun damu matuka kan rayuwar yarinyar shi yasa muka garzaya ofishin kwamishanan yan sanda, wanda ya tuntubi jami'ansa. Muna farin cikin dawo da ita."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel