Shuwagabannin Arewa ne matsalar Arewa – Hakeem Baba Ahmad

Shuwagabannin Arewa ne matsalar Arewa – Hakeem Baba Ahmad

Guda daga cikin shuwagabannin kungiyar dattawan Arewacin Najeriya, Dakta Hakeem Baba Ahmed ya fallasa mutanen dake mayar da agogon baya ga cigaban Arewa, inda yace shuwagabannin Arewa ne matsalar Arewa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Hakeem ya bayyana haka ne yayin wani taron kaddamar da reshen dalibai na hadaddiyar kungiyar kungiyoyin Arewa a jami’ar Bayero dake jahar Kano, inda yace shuwagabannin Arewa basu damu da cigaban yankin ba.

KU KARANTA: Allah raya jahar Katsina: Gwamnoni 10 da suka mulki jahar Katsina tun 1987

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa: “Mutanen dake shugabantar Arewanmu a yau basu da kwarewa a shugabanci, kuma basu shirya ma shugabanci ba, illa kawai suna son mulki da hanyar samun makudan kudade. Wannan ne yasa miyagun ayyuka suka yawaita a tsakaninmu, talauci, tumasanci da kuma cin mutuncin da muke fuskanta daga sauran yankunan kasar nan.”

Haka zalika Hakeem ya yi kira ga al’ummar yankin Arewa su kalli bambamcen bambamcen dake tsakaninsu a matsayin wata muhimmiyar jari da zasu iya amfani da ita wajen samar da cigaba a tsakaninsu, ba wai abin kyama ba.

“Arewa ta Musulmai ce, Arewa ta kirista ce, Arewa ta manyan kabilu ce, Arewa ta kananan kabilu ce, Arewa ta masu karfi ce, Arewa ta gajiyayyu ce. Arewa halittar Allah ne.” Inji shi.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban taron, Alhaji Bashir Tofa ya bayyana Arewa a matsayin jigo a siyasar Najeriya, don haka yace Arewa ba za ta taba gajiyawa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummarta ba.

A wani labarin kuma, a ranar 23 ga watan Satumba na shekarar 1987 ne gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kirkiro jahar Katsina daga cikin jahar Kaduna, wanda hakan yasa a yau Katsina ta cika shekaru 32 da kirkira.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel