Tirkashi: An kama mata da miji a lokacin da Suke yunkurin Shiga da kwaya ta sama da £2m kasar Ingila

Tirkashi: An kama mata da miji a lokacin da Suke yunkurin Shiga da kwaya ta sama da £2m kasar Ingila

Hukumomin kasar Pakistan sun kama wani mutum mai suna Mohammed Tahir Ayaz dan shekaru 26, tare da matarsa Ikra Hussain yar shekara 20, daga Huddersfield, West Yorkshire a filin jirgin sama na Sialkot.

An tattaro cewa suna iya fuskantan hukuncin kisa ko zaman kurkuku har karshen rayuwarsu bayan zargi da aka yi musu na yunkurin shiga da miyagun kwayoyi na kimanin £2m kasar Amurka.

A cewar yan sandan, ma’auratan suna shirin tashi daga Pakistan ta Dubai zuwa kasar Amurka. An kama su ne yayin da suke yunkurin hawa jirgin kamfanin Emirates Airlines a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba.

Tirkashi: An kama mata da miji a lokacin da Suke yunkurin Shiga da kwaya ta sama da £2m kasar Ingila
Tirkashi: An kama mata da miji a lokacin da Suke yunkurin Shiga da kwaya ta sama da £2m kasar Ingila
Asali: Twitter

The Mail Online ta rahoto cewa yan sandan, sun gano kimanin kilogram 25 na kwayoyin a boye cikin rigunan mata. An rarraba kwayoyin cikin riguna da yawa.

Jami’an sun fitar da jakkunan dake dauke da kwayoyin inda suka daura a ma’auni don awo. Sai aka samu kwayoyi mai nauyin kilogiram 25.

KU KARANTA KUMA: An kama makasan wani dan siyasan kasar

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Jami’an yan sandan jihar Lagas sun kama wasu mata biyu da suka kware wajen siyar da jarirai sabbin haihuwa a yankin Ejigbo da ke Lagas.

Anyi zargin cewa masu laifin sun siyar da jarirai 50 a tsakanin N500,000 da naira miliyan daya.

Wasu fusatattun matasa na gab da far ma masu laifin, Florence Nkem Douglas da Gift Micheal lokacin da yan sanda suka shiga lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel