Kyan alkawari cikawa: Gwamna El-Rufa'i ya kai yaronsa makarantar gwamnati (Hotuna)
Kamar yadda yayi alkawari a shekaru biyu da suka gabata, gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i, ya shigar da yaronsa, Abubakar Al-Siddique El Rufa'i, makarantar gwamnatin Kaduna Capital School dake unguwar Malali Kaduna.
Gwamnan tare da amaryarsa sun kai Abubakar mai shekaru 6 da haihuwa makarantar inda zai yi karatun firamarensa.
Wanna labari ya bayyana ne da safiyar Litinin a shafin ra'ayi da sada zumuntar fadar gwamnan jihar inda tace:
"A ranar 28 ga Disamban 2017, Malam Nasir El-Rufa'i yace ' Ni da kaina zan tabbatar da cewa yarona da zai isa shekaru shida a 2019, zan kaishi makarantar gwamnati a jihar Kaduna, idan Allah ya yarda."
"Kawo sauyi bangaren ilimin jihar Kaduna ijtihadi ne zamu cigaba da yi bayan shekarun da aka gurbatashi. Gwamnatin El-Rufai ta lashi takobin gyara makarantun gwamnati da kuma farfado da mutuncinsu ta yadda masu kudi kadai zasu rika kai yaransu makarantan kudi."
Kalli hotunan:

Asali: Facebook
KU KARANTA: Rufe iyakokin Najeriya ya hana fasa kwabrin man fetur kimanin lita milyan 11

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng