Wata tsohuwa ta shiga tasku bayan kamata da laifin siyar da wayan sata

Wata tsohuwa ta shiga tasku bayan kamata da laifin siyar da wayan sata

Jami’an yan sanda sun kama wata tsohuwa yar shekara 54, Hannah Ibadin, kan laifin syar da wata wayar sata kirar Nokia mallakar wani malamin cocin Katolika, Rev. Fr. David Aronokhale.

Wasu yan fashin da suka kwace masa mota kirar Toyoto Highlander ne suka sace harda wayar tasa.

Daya daga cikin yan fashin, Miracle Okon, ne ya ba Hannah wacce aka fi sani da Area Mama wayar, a wani wajen shaye-shaye da siyar da miyagun kwayoyi da ke unguwar Akpakpava.

Hannah tace ta kan ziyarci wajen shaye-shayen domin shan ganye kuma cewa bata san wayar sata bane.

Tace ta siyar da wayan akan N12,000.

A cewar Hannah, “Na hadu dashi a wajen shaye-shaye a unguwar Akpakpava. Ana kiran wajen da mahadar Nosa. Yana nan kafin a kai ofishin tura sako. Na bashi kudi sannan ya bani. An san wayar sata bane. Na je shan wiwi ne awajen. Mijina na a Uromi. Miracle yace yana zuwa shan wiwi a mashayar."

KU KARANTA KUMA: An kashe mutane 2, an raunata soja da farar hula 5 a sabon hari a Adamawa

Kwamishinan yan sandan jihar, Danmallam Abubakar yace za a gurfanar da masu laifin a kotu ba da jimawa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel