Rundunar soji ta saki lambobin da za a kira idan aka gano tserarrun yan ta’addan Boko Haram

Rundunar soji ta saki lambobin da za a kira idan aka gano tserarrun yan ta’addan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa wasu yan ta’addan Boko Haram da suka rage na neman mafaka a gidajen wasu mutane a wasu yankunan jihohin Borno da Yobe.

Kanal Ado Isa,kakakin operation lafiya dole a ranar Asabar, 21 ga watan Satumba, yace bayanai abun dogaro da ke iso ma rundunar ya nuna cewa yan ta’addan na tserewa sannan suna samun mafaka a gidajen wasu mutane a Maiduguri, Damboa, Gajiram, Monguno, Damasak, Biu, Gwoza Dikwa, Benisheikh, Ngamdu, Bama, Gamboru, Konduga, Gajigana da wasu kananan garuruwa a jihar Borno.

Yace wasu yan ta’addan kuma sun gudu zuwa Damaturu, Gujba, Buni Yadi, Buni Gari, Gashua, Kanamma, Yususufari, Goniri da Kukareta a jihar Yobe da sauran su.

Rundunar ta gargadi masu boye tserarrun yan ta’addan su kai rahoto ko kuma su mika su ga rundunar ba tare da bata lokaci ba ko kuma su fuskanci duk abunda ya biyo baya kan rashin aikata hakan.

KU KARANTA KUMA: Jiragen soji sun yi kasa-kasa da maboyar yan ta’adda, an kashe da dama a Borno

Kanal Ado Isa yace yayinda ake kokarin ganin an kama tserarrun yan ta’addan, ya bukaci yan Najeriya musammab wadanda ke zama a wadannan yankunan da ake magana da su kai rahoton duk wani bakon fuska da basu yarda dashi ba a garuruwansu.

“Ana rokon jama’a da su kai rahoton wadannan mutane ta shafin mu na ko ta wadannan lambar 193 (ana iya amfani da kowani layi) ko wadannan lambobin wayan: +2347017222225, +2348077444303, +2348099900131 and +2349060005290. Dan Allah ku kawo rahoton wadannan mutane kafin su kashe ku," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel