Tubabban 'yan ta'addan jihar Zamfara sun mika bindigogi 100 ga jami'an tsaro

Tubabban 'yan ta'addan jihar Zamfara sun mika bindigogi 100 ga jami'an tsaro

- Hukumar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ta samu bindigogi 100 daga tubabbun 'yan ta'adda

- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayyana cewa bindigogin na gargajiya ne amma masu matukar hatsari

- Tubar da 'yan ta'addan sukai ta biyo bayan goyon bayan da gwamnatin jihar ta baiwa jami'an tsaro da 'yan sandar jihar

Hukumar 'yan sandan jihar Zamfara sun samu bindigogi 100 daga wajen 'yan ta'addan da suka aje makamai a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da suka yi a hedkwatar hukumar da ke Gusau a ranar juma'a.

Kwamishinan ya ce duk da makaman sun hada da bindigogin gargajiya wadanda suka yi kamanceceniya da AK 47, RPG, LMC da sauran manyan makaman kare dangi, makaman sun kasance masu matukar hatsari.

KU KARANTA: Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar

"Yawan bindigogin da suka ajiye na nuna farkon nasara ne,"

"Ajiye bindigogi 100 da tubabbun 'yan ta'addan suka yi na nuna cigaba ne ta fannin tsaro. Bindigogin duk na gargajiya masu kamanceceniya da AK 47 amma kuma masu hatsarin gaske." Inji kwamishinan 'yan sandan.

A wani cigaba na daban kuma, kwamishinan ya ce hukumar ta samu wasu miyagun makamai 49 daga tubabbun 'yan ta'addan da a da suka gallabi jihar.

Shugaban 'yan sandan ya ce wasu daga cikin kungiyoyin 'yan ta'addan da suka tuba a jihar sun biyo hanyar lumana da sasanci da Gwamna Bello Matawalle ya bullo dasu.

Ya ce makaman da aka mikasu daga 25 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Satumba sun biyo bayan kwarin guiwar da gwamnatin jihar ta baiwa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel