Kotun zabe ta tabbatar da nasarar 'yan majalisu uku a Sokoto

Kotun zabe ta tabbatar da nasarar 'yan majalisu uku a Sokoto

Kotun sauraron karrakin zabe na jihar Sokoto tayi watsi da karrakin da jam'iyyar PDP da 'yan takarar ta suka shigar kan 'yan majalisar jihar Sokoto uku da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan majalisar uku sun hada da Bello Idris mai wakiltan Gwadabawa ta Arewa, Abdullahi Garba mai wakiltar Gwadabawa ta Kudu da Abubakar Altine mai wakiltan Gada ta Yamma.

'Yan takarar na jam'iyyar PDP a zaben na ranar 9 ga watan Maris na 2019 sun hada da Habibu Mu'azu Gwadabawa ta Arewa, Nasiru Balarabe, Gwadabawa Ta Kudu da Tanimu Dangaladima, Gada ta Yamma.

DUBA WANNAN: An yanke wa tsohon shugaban kasar hukuncin shekaru biyu a gidan yari

Wadanda su kayi karar sunyi ikrarin ba a bi dokokin zabe ba yayin gudanar da zaben.

A yayin zartar da hukuncin kan zabukkan a ranar Juma'a, kotun tayi watsi da dukkan kararrakin saboda rashin kwararran hujojjoji.

Jagoran alkalan, Mai shari'a Peter Akhimie Akhihiero ya ce wadanda suka shigar da karar sun gaza gabatar da gamsassun hujojojji a gaban kotun.

Ya kuma ce a biya dukkan wadanda aka yi kara N20,000 kowannesu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel