'Yan kungiyar asiri sun halaka wani basarake a jihar Delta

'Yan kungiyar asiri sun halaka wani basarake a jihar Delta

- 'Yan kungiyar asiri a karamar hukumar Udu sun sokawa wani basarake wuka

- Babu bata lokaci aka kwashi basaraken zuwa asibiti inda ya ce ga garinku

- An sanyawa karamar hukumar Udu ta jihar Delta dokar ta baci sakamakon fadace-fadacen 'yan kungiyoyin asiri da ke addabar yankin

Duk da dokar hana yawo da aka saka a karamar hukumar Udu ta jihar Delta don kawo karshen kungiyoyin asirin da suke baje kolinsu a yankin, an samu rahoton kashe wani basarake mai suna Egolor Kolo.

An kashe basaraken Dan yaren Urhobo a ranar Alhamis a Ukpiovwin cikin garin Udu da karfe 8:00 na yamma.

"Fada mai tsanani ya tashi Inda har aka kai ga sokawa mamacin wuka duk da dokar ta bacin da aka sanya," inji jaridar TribuneOnline.

Majiyarmu ta gano cewa, bayan an soki basaraken da wuka, an kwashesa zuwa asibiti inda ya ce ga garinku.

KU KARANTA: Soyayya ruwan zuma: Ya kashe kansa sakamakon rashin nasarar samun soyayyar wata budurwa

Wani babban jami'in 'yan sandan Najeriya ya sanar da jaridar TribuneOnline cewa salon cajen da jami'an tsaro ke yi don zakulo 'yan kungiyar asiri a karamar hukumar ba zai yi aiki ba.

Ya ba jami'an tsaro shawarar su je har gidajen 'yan kungiyar asirin ne don zakulo su. Tsayawa kan titina tare da caje ba zai kawo karshen matsalar ba.

Idan zamu tuna, shugaban karamar hukumar Udu, Jite Brown, a makon da ya gabata ya sanya dokar ta baci a karamar hukumar don kawo karshen fadace-fadacen 'yan kungiyar asiri a yankin.

Yankunan da dokar ta bacin ta shafa sun hada da birnin Ovwia, Ekete cikin gari, Ekete ta yankin ruwa, birnin Owhase, Orhuwhorun junction, Express Junction da Mofor Junction.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel