Mugunta ruwan fakko: Uwargida ta kashe jaririn kishiyarta da fiya fiya

Mugunta ruwan fakko: Uwargida ta kashe jaririn kishiyarta da fiya fiya

Wata mata yar shekara 22, Harela Uba ta shiga hannun Yansandan jahar Neja bayan ta shayar da jaririn kishiyarta wanda bai wuce kwanaki 3 a duniya ba kacal gubar fiya fiya, inda take ya zamto matacce, inji rahoton jaridar Blue Print.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Harela ta aikata wannan ta’asa ne a ranar 14 ga watan Satumba a gidansu dake kauyen Shakodna cikin karamar hukumar Shiroro na jahar Neja, kuma mijinta, Uba Saidu ne ya kai karar matarsa tasa da kansa ga Yansanda.

KU KARANTA: CBN ta ware naira biliyan 30 domin habbaka noman kwakwan manja a Najeriya

Ita dai Harela wanda ita kanta tana dauke da ciki wata 8 ta baiwa diyarta mai shekaru 7 fiya fiyan ne ta shayar da jaririn kishiyarta, yayin da kishiyar mai suna Fa’iza Uba ta bar jaririn a dakinta ta shiga cikin bandaki tana wanka.

Sai dai a lokacin da ta fito daga bandakin sai ta tarar farin kumfa a bakin jaririn, a nan ta kwantsama ihu nan da nan aka garzaya da jaririn zuwa asibiti, amma ko kafin a isa a asibitin ya cika. Kaakakin Yansandan jahar, Mohammed Abubakar ma ya tabbatar da aukuwar lamarin.

“Mun gayyaci uwargidar Malam Uba Saidu, Harela sakamakon ita kadai ce a gida a lokacin da lamarin ya auku, domin mu yi mata tambayoyi, a yayin da take amsa tambayoyinmu ne ta tabbatar mana da cewa ita ta aiki diyar yar shekara 7 mai suna Khadija da fiya fiya domin ta shayar da jaririn Fa’iza.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yace za su gurfanar da Harela gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

A wani labarin kuma, Yansanda sun kama wasu mutane guda 7 daga cikin ‘Yan kwamiti’ da jami’an hukumar Hisbah da laifin kashe wani mutumi mai suna Ibrahim A Ibrahim sakamakon suna zarginsa da sace budurwarsa Maryam Salmanu dake garin kontagora.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: