Kotu ta yankewa saurayi hukuncin watanni 4 a gidan maza akan satar kaji

Kotu ta yankewa saurayi hukuncin watanni 4 a gidan maza akan satar kaji

- Babbar kotun yankin Mpape ta yankewa Yusuf Jimidi hukuncin watanni 4 a gidan maza

- Alkalin ya yanke hukuncin ne sakamakon satar kaji biyar da saurayin ya yi

- An yankawa saurayin N15,000 da zai biya mai kajin

Babbar kotun yankin Mpape da ke Abuja ta yankewa wani manomi wata hudu a gidan yari.

Mutumin mai suna Yusuf Jimidi Dan shekaru 19 ya saci kaji 5 ne mallakin wani mai tireda.

Mai shari'a Hassan Muhammad ya yanke hukuncin ne bayan Jimidi ya amsa laifinsa.

Muhammad ya baiwa wanda ake tuhumar damar biyan N10,000 ko kuma watanni hudu a gidan maza.

KU KARANTA: Kotu ta yanke hukuncin kwace kadarorin kamfanin P&ID

Mai shari'ar ya umarci mai laifin da ya biya N15,000 ga mai kara, Aremo Folorunsho.

Tun farko Dan sandan da ya gabatar dasu gaban kotu, M. Austin ya sanar da kotun cewa mai karar ya kawo kokensa ga ofishin 'yan sanda na Mpape da ke Abuja a ranar 16 ga watan Satumba.

Austin ya ce mai laifin ya saci kaji biyar ne masu darajar N15,000.

Ya ce bayan da 'yan sanda suka tuhumesa, ya amsa laifinsa.

Laifinsa kuwa ya saba wa sashi na 288 na dokar Penal Code.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel