Ke duniya: Banga aibun shan wiwi ba, in ji yaro dan shekaru 12

Ke duniya: Banga aibun shan wiwi ba, in ji yaro dan shekaru 12

- Rundunar 'yan sanda ta musamman ta jihar Legas ta cafke mutane 71 da zargin laifuka da dama

- A cikinsu kuwa harda dan shekaru 11 da ya ce bai ga illar shaye-shaye ba

- Karamin yaron ya ce ya fara kora miyagun kwayoyin ne tun yana da shekaru 9 a duniya

Rundunar 'yan sanda ta musamman ta jihar Legas ta cafke Dan shekaru 11 mai suna Hamed Gilani a samamen da ta kai Oshodi.

Hamed Gilani, ya sanarwa da 'yan sandan cewa bai ga wani aibun shan wiwi ba gani da cewa yana sha tun shekarunsa 9.

Gilani na daya daga cikin mutane 71 da rundunar 'yan sandan ta kama a safiyar jiya yayin samamen da ta kai wajen titin jirgin kasa da ke Oshodi, a tsakiyar birnin Legas.

"Kawuna na titi ne ya fara nunamin shaye-shaye lokacin da fara kwana kasan gada kuma ina masa aike-aike," in ji shi.

KU KARANTA: Alkalin alkalan Najeriya zai rantsar da sabbin manyan lauyoyi a kotun koli

Gilani ya bayyana cewa ya zo Legas ne daga jiha mai makwaftaka da garin Legas bayan iyayensa sun rabu.

Suraju Ademola, wanda ake zargi da fashi da makami, an kamasa yayin samamen. Ya bayyana cewa yana daga cikin 'yan fashin da suka shahara a kwacewa mutane dukiyarsa a wajen gadar Oshodi.

Ademola ya ce, ya yi watanni 7 yana kwana a kasan gadar.

Shugaban rundunar, Olayinka Egbeyemi, wanda ya jagoranci samamen, ya ce an samu wasu daga cikin bata garin da miyagun kwayoyi irinsu Codein, wiwi da tramadol.

Egbeyemi ya tabbatar da cewa duk wasu guraren da aka san bata garin na zama za a zaga su don kamosu tare da hukuntasu.

Ya ce an saki mutane 13 a cikin wadanda aka kaman bayan an gano basu da hannu.

"Gilani ne kadai karami a cikinsu. An kuma turasa gidan gyaran hali na jihar Legas din don daukar matakin da ya dace," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel