An kama 'yan banga 5 a kan kisar Ibrahim Ibrahim

An kama 'yan banga 5 a kan kisar Ibrahim Ibrahim

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Neja ta kama mambobin kungiyar 'yan banga biyar a garin Kontagora da ake zargi da laifin azabtar da wani bawan Allah har sai da ya mutu abinda 'yan sandan suka ce zalunci ne.

Mutum uku cikin wadanda aka kama 'yan Hisba ne yayin da sauran biyun 'yan kungiyar banga ta Yankumiti ne. An yi ikirarin cewa mutanen biyar sun azabtar da wani Ibrahim A. Ibrahim har ya mutu kan wani rashin jituwa kamar yadda Linda Ikeji's blog ya ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Adamu Usman ya tabbatar da kama mutanen biyar da suka hada da Ahmadu Yahaya, 35; Dahiru Abdullahi, 28; Abdulrasheed Atabo, 20, ('Yan Hisba) sai kuma Yakubu Usman, 25, and Yunusa Adamu, 24, 'yan kungiyar banga ta Yankumiti.

Ya kuma ce wadanda suka kashe din dan asalin garin Unguwan Yamma ne a karamar hukumar Kontagora.

DUBA WANNAN: An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi

"Anyi ikirarin cewa wanda aka kashe din ne ya sace wata Maryam Salmanu da ke zaune a Unguwan Yamma a karamar hukumar Kontagora da ake kyautata zaton budurwar daya daga cikin wadanda ake zargin ne," inji shi.

Kwamishinan 'yan sandan ya yi bayanin cewa wadanda ake zargin sun gayyaci Ibrahim da wasu mutuane biyu, Musa Salahu da Ahmed Mohammed zuwa ofishin su da sunan bincike kan sace yarinyar inda suka yi musu duka amma daga bisani suka saki mutane biyu amma suka rike marigayin.

Kwamishinan ya cigaba da cewa, "Yayin da wadanda ake zargin suka lura cewa marugayin ya galabaita sosai sai suka mayar da shi dakinsa misalin karfe 2 na dare ta tare sun sanar da 'yan uwansa ba. Duk da cewa daga baya 'yan uwansa sun yi yunkurin kai shi asibiti da suka gano an dawo da shi, ya mutu misalin karfe 3 na dare."

Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike kuma ya yi kira da 'yan banga na jihar su rika aiki kamar yadda doka ta tanada wurin talafawa 'yan sanda ba tare da wuce gona da iri ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel