Shari'ar Abba gida-gida da Ganduje: Alkali ta ce hukuncinta ba zai zama 'inconlusive' ba

Shari'ar Abba gida-gida da Ganduje: Alkali ta ce hukuncinta ba zai zama 'inconlusive' ba

- Mai shari'a Halima Shamaki, ta ce ita ba za ta ce hukuncinta bai kammalu ba kamar INEC

- Mai shari'ar ta ce tana sane da kwanaki 180 da dokar zabe ta gindaya kuma hukuncin zai bayyana kafin lokacin

- Lauyan Ganduje ya ce sai dai in PDP za ta samo kuri'un kowanne akwatin zabe, hakan kadai ne zai tabbatar da nasarar Dan takararsu

Shugabar alkalan shari'ar Abba Kabir Yusuf da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Halima Shamaki, a ranar Laraba ta ce, ita ba za ta ce hukuncinta bai kammalu ba kamar yadda INEC ta yi a zaben jihar.

Shamaki ta ce, ta na sane da kwanaki 180 da dokar zabe ta bada, don haka za ta kammala aikinta tare da fidda hukuncin kafin cikar kwanakin.

KU KARANTA: Magu ya fadawa tsohon ministan shari'a ya gurfanar da kansa gaban kotu

A yayin zaman kotun, duk lauyoyin wadanda ake kara, Ofiong Ofiong, Alex Ezinyon da Ahmed Raji sun toki kotun da ta yi watsi da karar domin lauyoyin wadanda su ka yi karar sun kasa tabbatar da zargin da su ke.

Masu kara da lauyansu, Kanu Agabi, ya ba da dalilinsu na cewa hukumar zabe mai zaman kanta bata gudanar da zaben gaskiya ba a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Agabi ya kara jaddada cewa hukumar INEC da kanta ta sanar cewa Dan takarar jam'iyyar PDP ne a gaba yayin da ake tattara kuri'u da sanar da sakamako.

Daga baya ne, INEC ta yanke shawarar soke kuri'un mazabu 207 wanda yaci karo da doka.

"INEC ta sanar da sakamakon zaben ranar 9 ga watan Maris,2019. A garemu wannan shari'ar mai sauki ce, abinda muke fatan kotun nan ta yi shine tabbatar da wanda ya ci zaben nan a matsayin mai nasara," in ji shi.

Hakazalika, lauyan Ganduje, Ofiong Ofiong, ya musanta nasarar PDP a zaben 9 ga watan Maris din. Ya ce sai dai in jam'iyyar za ta samar da kuri'un kowanne akwatin zabe na jihar.

Bayan tafka muhawarar, Mai shari'a Shamaki ta daga zaman kotun.

A halin yanzu dai, kotun na da kwanaki 22 da suka rage don yanke hukunci tsakanin Abba Yusuf na jam'iyyar PDP da Ganduje na jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel