Hukumar makaranta ta hana yarinya mai shekaru 14 shiga aji saboda girman jikinta
- Hukumar makaranta ta tirsasa Kada Jones mai shekaru 14 zama ita kadai ko ta koma gida
- Shugaban makarantar ta fadi hakan ne sakamakon girman jikin yarinyar wanda ya kaita ga yin bujen da ya zarta na kowa girma
- Kada ta nuna damuwarta matuka akan tsangwamarta da aka yi bayan bata aikata wani laifi ba
Hukumar makarantar Portchester Community School da ke Fareham, Hants ta tirsasa Kada Jones mai shekaru 14 a duniya da zama ita kadai ko kuma zaman gida sakamakon girman da tayi da kayan makaranta.
Kada, wacce ta koma hutu don fara zangon karatu na farko, ta sanya buje wanda ya saba da kayan makarantar sakamakon girman jikinta.
Yarinyar mai shekaru 14 ta ce irin girman bujen da ta sanya shekarar da ta gabata ne kuma hukumar makarantar baau yi magana akai ba.
Hukumar makarantar ta bukaci yarinyar da ta kiyaye dokar sanya kayan makarantar ko kuma ta koma gida.
KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidan shakatawar gwamna, dan majalisa da gidaje 300 a jihar Anambra
Shugabar makarantar tace girman bujen ya wuce misalin yadda suke bukatar kayan makaranta ya kasance don haka ne zasu iya cewa Kada ta take dokar makarantar.
Faruwar abin ta dami yarinyar inda ta ce ita bata san laifin da ta yi ba har ake kyararta.
"Nayi kuka na kusan kwanaki biyar da suka gabata. Ban san laifin da na yi ba. Ana ware mutum ne idan ya yi laifi; suna ta kyarata kamar ba mutum 'yar uwarsu ba. Ni inason zuwa makaranta," inji ta.
Mahaifiyarta Carleen Jones ta ce diyarta garau take kuma abin na damunta. Bujen da diyarta ta sanya kusan iri daya ne da wanda makarantar ta bukata, banbancinsu kawai girma da tsayi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng