Wani sarki ya koka kan yadda dandalin sada zumunta ke janyo fitina a garin sa

Wani sarki ya koka kan yadda dandalin sada zumunta ke janyo fitina a garin sa

Sarkin garin Ekwulobia da ke karamar hukumar Aguata na jihar Anambra, Igwe Emmanuel Onyeneke a ranar Talata ya ce kafar sada zumunta na suka sa har yanzu rikicin da ke masarautarsa ta ki ci taki cinye wa.

Ya ce 'yan adawa a garin suna amfani da dandalin sada zumunta wurin yada kiyaya da tsauraran ra'ayoyi hakan yasa har yanzu rikicin da ya ke karewa.

Ya ce farfagandar da ake ta yadawa a dandalin sada zumunta ne suka sa har yanzu rikicin ya ki kare wa.

Onyeneke ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a fadarsa domin jana'izar farai ministan garin Ekwulobia, Dakta Gabriel Ezeukwu.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace kujerar dan majalisa PDP a jihar Sokoto, ta bayar da umurnin yin zaben raba gardama

Sarkin ya yi bakin cikin yadda farai ministan ya rasu ba tare da ganin an samu zaman lafiya a garin ba duk da irin namijin kokarin da ya yi na samar da zaman lafiyar.

Ya yi ikirarin cewa wani mutum da ke amfana daga rikicin ya karkatar da fiye da naira miliyan 100 daga kudin al'ummar garin.

Ga wani sashi daga jawabin da Sarkin ya yi ,"'Yan adawa a garin nan sun kafu ne tun lokacin da aka kafa kungiyar cigaba na garin nan shekaru 80 da suka shude.

"Tarihi ya nuna cewa mutanen garin Ekwulobia sun ci mutuncin shugaban kungiyar cigaba marigayi Cof Gabriel Nnaike na garin Umuchiana.

"Tun wannan lokacin lamarin bai sauya zani ba. Mutanen Ekwulobia sun cigaba da cin mutuncin shugabanin kungiyar cigaban kuma yanzu da intanet ya samu abin ya dauki sabon salo."

Ya ce gwamnatin jihar Anambra tayi kokarin yin sulhu tsakaninsu kuma ta amince da shugabancinsa amma shugaban 'yan adawan ya ki amincewa da hakan saboda kudin da ya ke samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel