Na rasa yadda zanyi da ita saboda har cikin dakin mu na sunnah Madina take kawo gardi tayi zina dashi - Wani mutumi ya koka

Na rasa yadda zanyi da ita saboda har cikin dakin mu na sunnah Madina take kawo gardi tayi zina dashi - Wani mutumi ya koka

- Wani mutumi mai suna Tayo Owoloye ya nemi kotu ta raba auren shi da matarsa wacce suka shafe shekara 11 suna tare

- Mutumin ya nemi kotun ta raba auren ne bayan ya bayyana dalilai masu yawa na irin cin amanar shi da take yi

- Ya bayyana cewa akwai 'yarsu mai shekara 11 da ta sanar da shi cewa akan idonshi mahaifiyarta take shigo da kato gida su shiga daki, kuma tasha kama su suna lalata

Wani mutumi dan shekara 35 wanda bashi da aikin yi, mai suna Tayo Owoloye, ranar Litinin dinnan da ta gabata ya bayyanawa wata kotu a jihar Legas cewa matar shi tana kawo saurayinta hr cikin dakinsu na sunna suna zina.

Owoloye wanda yake rokar kotu ta kawo karshen auren nasu wanda suka kwashe shekaru 11 suna tare da matar tasa mai suna Madinat, ya bayyana cewa 'yar su mai shekara 11 ta sanar dashi cewa mahaifiyarta tana kawo wani har cikin gidansu kuma ta sha ganinsu suna lalata.

"Na taba ganin hirar ta da wani mutumi mai suna Timothy a WhatsApp, dana tambayeta, sai tayi saurin goge hirar ta su, sai na kai kararta wajen 'yayunta mata guda biyu.

"Sannan kuma tana kwanciya da wani mutumi mai suna Stanley."

"Modinat ta zo wajen rasuwar mahaifiyata aa jihar Ondo, amma ko ta tsaya ta kwana bata yi ba, sai daga baya na gane ashe ta zo da Stanley ne, suka kama daki otel suka kwana tare.

KU KARANTA: Soyayya ko hauka: Tsananin soyayya ta saka budurwa sato akuyar makwabta ta yanka ta yiwa saurayinta farfesu

"Ina kauyen mu Modinat ta kirani a waya cewar bata da lafiya, kuma an kwantar da ita a asibiti a Legas, dana je asibitin washe gari sai wata ma'aikaciyar asibiti take fada mini cewa wani mutumi ya zo ya kwana da ita a asibitin, sai daga baya na gane cewa ashe Stanley ne.

"Dana je na samu Stanley ya bayyana mini cewa yana kwanciya da mata ta amma kuma ya nemi na yafe masa.

"Na sake duba Stanley a Facebook saboda ina so na san ko shi wanene, sai naga hotunansu shi da matata wanda suka dauka a cikin dakinmu na sunna akan gado."

Owoloye ya bai wa kotu shaidar hotunan da Stanley ya sanya a shafinsa na Facebook din wanda yake tare da matar tashi.

Sai dai da aka tambayi Modinat dalilinta na yin wannan aika-aika ta bayyana cewa ba ta son mijin nata ne yanzu ko kadan.

Alkalin kotun Mai shari'a Mr. Adeniyi Koledoye, bayan sauraron korafi daga kowanne bangare, ya roki ma'auratan da su zauna lafiya, inda kuma ya daga sauraron shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Satumbar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel