Yaro ya dabawa mahaifinsa wuka har lahira a jihar Kano

Yaro ya dabawa mahaifinsa wuka har lahira a jihar Kano

Wani matashi mai suna Habibu Ibrahim ya caccakawa mahaifinsa mai sune Malam Ibrahim Salihu mai shekaru 80 wuka har lahira a kauyen Asada, karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano.

Amma a ranar Talata, jami'an yan sanda sun bayyana cewa sun damke Habibu bayan ya arce daga garin.

Kakakin hukumar yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce daya daga cikin yan uwan Habibu, Yahaya Ibrahim, ya kai kara ofishin hukumar dake Doguwa a ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2019 cewa kaninsa ya cakawa mahaifinsu wuka cikin dare.

Ya ce: "Yayinda muka samu labarin, jami'an hukumar sun garzaya da shi asibitin Doguwa domin jinya amma ya mutu misalin karfe 6:30 na asuba."

Kakakin yan sanda ya ce bayan gudanar da binciken da ya kamata kan gawar, an mika ta ga iyalan domin jana'izarsa bisa ga koyarwan addinin Musulunci.

"Binciken da muka gudanar ya nuna cewa yaron dan kwaya ne kuma ya aikata wannan aika-aika ne bayan ya bugu da kayan maye."

"Yan'uwansa sun bayyana mana cewa Habibu ya dade yana ta'amuni da muggan kwayoyi kuma hakan ya kasance babban kalubale ga mahaifinsu har ya kai ga rasuwarsa." A cewar DSP Haruna

A karshe, ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu, ya bada umurnin mayar da bincikensa sashen leken asirin hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel