Yadda wata budurwa ta burma ma Saurayinta wuka, ta kashe shi har lahira

Yadda wata budurwa ta burma ma Saurayinta wuka, ta kashe shi har lahira

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas sun samu nasarar cafke wata buduwar yar shekara 23 mai suna Stella Peter wanda ta kashe saurayinta, Bala Haruna mai shekaru 25 a rayuwa.

Rahoton jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa Stella ta kashe Bala ne sakamakon takaddama ya barke a tsakaninsu a gidansu dake lamba 2, layin Tejuosho, cikin yankin Surulere na jahar Legas, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar, Bala Elkana ya tabbatar.

KU KARANTA: Hukumar NRC ta karyata rahoton harin yan bindiga a kan jirgin Abuja-Kaduna

Bala yace rikicin ya samo asali ne sakamakon tirjiya da saurayin Stella, Bala Haruna ya nuna wajen kin bata kudi domin ta shirya ma diyarsu yar gaba-da-fatiha bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan ne matsalar da ta sabbaba rikici tsakanin masoyan biyu dake zaman dadiro a jahar Legas, wanda har ta kai ga Stella ta dauki wuka ta burma ma Bala Haruna a ciki,nan take ya fadi matacce.

Tuni kwararrun Yansanda masu iya bincike a kan laifin kisan kai suka dauki gabaran gudanar da bincike game da kisan, haka zalika ita ma Stella ta amsa laifinta na kashe saurayinta Bala.

A wani labarin kuma, wani lamari mai tsananin muni ya faru a kauyen Asada na karamar hukumar Doguwa ta jahar Kano, inda wani matashi ya halaka ubansa dan shekara 80, Malam Ibrajim Salihu.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya bayyana sunan matashin, Habibu Ibrahim mai shekaru 35, sa’annan yace sun kamashi bayan ya tsere.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel