Yanzu-yanzu: An samu gawar wata budurwa a rataye a jikin bishiya a jihar Jigawa

Yanzu-yanzu: An samu gawar wata budurwa a rataye a jikin bishiya a jihar Jigawa

- Wani rahoto da muka samu ya nuna yadda aka iske gawar wata budurwa na lilo a jikin bishiya a jihar Jigawa

- An bayyana cewa har yanzu ba a san dalilin da ya sanya budurwar kashe kanta saboda bata bar takarda ko wata shaida ba

- Yanzu dai an dauke gawar budurwar zuwa asibiti domin cigaba da bincike

Wata budurwa ta kashe kanta a jihar Jigawa, an iske gawar budurwar ne a rataye tana lilo a jikin reshen bishiya da safiyar jiya Litinin 16 ga watan Satumbar shekarar 2019.

Har yanzu dai babu wanda ya san ainahin dalilin da ya sanya budurwar ta dauki wannan mataki, saboda bata bar wata shaida ko wasiyya dake nuni da dalilinta na kashe kan nata ba.

Kamar yadda jaridar LindaIkeji ta bayyana, yanzu haka dai jami'an tsaro sun dauke gawar budurwar inda suka kai ta wajen ajiye gawarwaki dake asibiti don lura da ita kafin su kammala bincike.

KU KARANTA: Allah daya gari ban-ban: Kabilar da saurayi zai shiga har gidan uban budurwa ya sace ta kafin daga baya yaje ya nemi iyayenta su aura masa ita

A Najeriya dai bayan kashe-kashe da 'yan ta'adda suke yi babu kama hannun yaro da kuma garkuwa da mutane da ake ta faman yi babu dare babu rana, yanzu haka kuma wannan masifar ta mutum ya kashe kanshi tana kara karfi.

Ana ta kara samun yawaitar matasa suna kashe kansu ta hanyar shan guba, ko rataye kansu ko kuma dai wani abu makamancin haka, inda akasari aka fi samun dalibai da aikata irin wannan abu saboda wasu dalilai nasu da suke rubutawa su bari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel