Kungiyar Malaman Najeriya za su shiga yajin aiki na dindindin

Kungiyar Malaman Najeriya za su shiga yajin aiki na dindindin

Hadaddiyar kungiyar malaman kwalejojin ilimi na Najeriya, COEASU, sun yi ma gwamnatin Najeriya barazana fadawa yajin aiki na dindindin matukar ba ta amince da bukatunsu ba, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyar ta yi wannan barazana ne sakamakon yin watsi da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninta da gwamnatin tarayya game da wasu muhimman bukatunta da ta mika ma gwamnati gabanin janyewar wancan yajin aiki da ta yi.

KU KARANTA: Taka leda: Najeriya za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta Brazil a Singapore

Shugaban kungiyar, Nuhu Ogirima tare da sakataren kungiyar, Taiwo Olayanju ne suka rattafa hannu a kan sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Talata, 17 ga watan Satumba bayan kammala taron kungiyar da aka daga ranar 10 zuwa 11 ga wata a Legas.

Sanarwar ta koma game da rikon sakainai kashi tare da nuna halin ko in kula da ministan ilimi yake nunawa game da bukatun malaman, sa’annan ta caccaki hukumar gwamnatin tarayya dake kula da kwalejojin ilimin kasar nan.

Amma duk da haka Ogirima ya bayyana cewa tunda dai shugaban kasa ya sake nada Adamu Adamu a matsayin sabon ministan ilimi, yana sa ran zai sake duba bukatunsu tare da yin abinda ya kamata.

Daga karshe Ogirima ya gargadi ma’aikatar ilimi da hukumar kula da kwalejojin ilimi na Najeriya da su dauki matsalolin kungiyar malaman kwalejojin ilimi da muhimmanci, idan kuma ba haka zasu daka yajin sai baba ta ji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng