Maganin damfara: Hanyoyi 5 da mutum zai gane kudin jabu

Maganin damfara: Hanyoyi 5 da mutum zai gane kudin jabu

'Yan Najeriya da dama sun sha fada wa hannun 'yan damfara saboda basa iya banbance wa tsakanin takardun kudin jabu da masu kyau.

Ga wadanda hakan ta taba faruwa da su da kuma wadanda ma hakan bata faruwa garesu ba, ga hanyoyin da za a iya bi domin gane takardun Naira marasa kyau.

1. Ta hanyar taba takardun kudi

Idan ka rike takardar Naira sai ka ji ta cika laushi kamar takarda ko kuma hoton dake jikin kudin bai fito sosai ba, to gaggauta mayar ewa wanda ya baka.

2. Za a iya amfani da ruwa

Idan mutum bai gamsu da takardun kudin da aka bashi ba, zai iya jika hannunsa da ruwa sannan ya taba takardar kudin ko kuma ya goga su a cikin hannunsa mai laima, idan kudin na jabu ne, zai ga kalarsu ta fara fice wa.

Idan hakan bai wadatar ba, mutum zai iya saka takardar kudin a cikin ruwa na tsawon dakika 30 (30 seconds), da zarar ka ga kalarsu ta fara canja launin ruwan to marasa kyau ne, saboda ruwa baya wanke kalar takardun kudi masu kyau.

3. Ankare wa da wani hatimi mai launin gwal

Takardar N1000 na dauke da wani hatimi a gefen sa hannun gwamnan CBN. Hatimin jikin jabun kudi yana fice wa idan aka kankare shi ko kuma idan kudi ya sha wuya a hannun jama'a.

Idan hanyoyi biyu da aka ambata a sama sun yi a mutum wuyar aikata wa, zai iya gwada kankare hatimin mai launin gwal koda da farcen yatsansa ne.

DUBA WANNAN: Korafin Aisha Buhari: EFCC ta fara binciken a kan tafka badakala a cikin shirin NSIP a jihohin arewa 2

4. Yin duba na tsanaki a kan wani zare mai sheki a jikin takardun kudi

Akwai wani zare mai sheki a jikin kowacce takardar kudin Naira amma banda N50. Zaren yana da tsayi daidai da kowacce takardar Naira.

Zaren na da kauri kuma za a iya jinsa a hannu idana aka taba takardar kudi. Ya fi bayyana a jikin tsofin kudi, amma zaren bashi da kauri a jikin jabun kudi kamar na jikin kudi masu kyau. Sannan yana saurin kankaru wa a jikin takardun kudi na bogi.

5. Ta hanyar amfani da kwan lantarki masu dauke da sindarin 'mercury'

Akwai wasu abubuwa a jikin takardun kudi da ido ba ya iya ganinsu ba tare da taimakon kwan wutar lantarki masu dauke da sinadarin 'mercury' ba. Kowacce takardar Naira mai kyau na dauke da su.

Idan mutum ya kalli takardar N1000 a hasken kwan lantarki mai sinadrin 'mercury', zai ga an rubutu 1,000 da lambobi a kwance a jikin takardar, amma idan takardar kudin ta jabu ce, zai ga komai a juye (upside down).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel