Yanzu-yanzu: Buhari yana zaman sulhu tsakanin IGP da PSC kan daukan sabbin yan sanda

Yanzu-yanzu: Buhari yana zaman sulhu tsakanin IGP da PSC kan daukan sabbin yan sanda

Shugaba Muhammadu Buhari yana zaman sulhu tsakanin sifeto janar na hukumar yan sanda, IGP Mohammed Adamu, da shugaban ma'aikatar aikin yan sanda, Musiliu Smith, a fadar shugaban kasa dake Villa, Abuja.

Smith da kansa tsohon sifeto janar na hukumar yan sanda ne kafin murabus.

Ya shiga ganawa da Buhari tare da wasu jami'an ma'aikatar.

Hakazalika shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, na cikin ganawar.

A farkon wannan watan, hukumar kula da yan sanda PSC ta yi fito na fito da sifeto janar IG Adamu kan shin wanene ke da hakkin daukan sabbin jami'an yan sanda 10,000 da shugaba Buhari yayi umurni.

Rahotanni sun bayyana cewa an dakatad da daukan sabbin yan sanda sai sun sasanta.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta gano 'yan kwangila 1,723 da suka karba N70b suka yi muqus

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, a jawabin da ya saki ya tabbatar da cewa an dakatad da daukan yan sandan.

Ya umurci matasa masu neman aikin su saurari sakamakon da zai biyo baya kuma su yi watsi da wani jerin sunaye da aka fitar saboda ba sahihi bane.

Ikechukwu Ani ya bayyana cewa duk wanda yayi kokarin daukan yan sanda yanzu na kokarin fito na fito da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel